Faransa ta ki janye jakadanta daga Nijar duk da wa'adin da sojoji suka ba shi./Hoto: AA

Faransa ta umarci sojojin Nijar su yi gaggawar sakin wani mai bai wsa 'yan kasarta shawara da ke kasashen waje.

Ta bayar da umarni ne ranar Talata a wata sanarwa da ta fitar.

"Faransa tana bibiyar halin da Stephane Jullien, mai bayar da shawara ga 'yan kasarmu da ke Nijar, yake ciki sau da kafa. Jami'an tsaron Nijar ne suka kama shi ranar 8 ga watan Satumba, kuma muna kira a yi gaggawar sakinsa," in ji sanarwar da Ma'aikatar Wajen Faransa ta fitar.

Ta kara da cewa an sanya jami'ai cikin shirin ko-ta-kwana domin su tabbatar da “tsaron 'yan kasarmu” tun da aka yi juyin mulki.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun umarci 'yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga kasar

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da Nijar tun ranar 26 ga watan Yuli lokacin da Janar Abdourahamane Tchiani, tsohon mai tsaron fadar shugaban kasa, ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

Kwanakin baya sojojin sun umarci jakadan Faransa da ke Nijar su fice daga kasar.

Sai dai Faransa ta yi fatali da umarnin, tana mai cewa sojojin da halastattun masu rike da mukamai ba ne.

AA