Sojojin Faransa a tsaye kusa da motocin sulke a sansanin sojin Faransa na Port-Bouet da ke Abidjan. / Hoto: AFP

Faransa a ranar Alhamis ta janye daga sansani ɗaya da take da shi a ƙasar Ivory Coast da ke Yammacin Afirka, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito.

Ministan Tsaron Fatansa Sebastien Lecornu a hukumance ya halarci bikin rufe sansanin. Ivory Coast ko kuma Côte d'Ivoire, ƙasa ce da a baya ke ƙarƙashin ikon Faransa.

A halin yanzu za ta ci gaba da haɗa kai da Faransa ta ɓangaren aikin soji, kamar yadda a baya Ministan Tsaron Ivory Coast Tene Birahima Ouattara ya sanar.

Sansanin da ke Port-Bouet wanda ke a kusa da babban birnin ƙasar Abidjan, za a mayar da sunansa sansanin Thomas d'Aquin Ouattara, wato sunan shugaban sojin ƙasar na farko.

Raguwar tasirin Faransa

Sojojin Faransa a nahiyar Afirka na ci gaba da raguwa a 'yan shekarun nan bayan da kasashen yankin da suka hada da Chadi da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso suka fatattaki sojojin da suka yi wa ƙasashen mulkin mallaka a baya.

A halin yanzu dai sojojin Faransa na ci gaba da zama a kasashen Djibouti da Gabon, kasashen biyu da ba su nuna sauye-sauye ga yarjejeniyoyin da suka kulla da Paris kan kasancewar sojojinta ba.

AA