Faɗan da aka gwabza tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai ya yi sanadiyyar mutuwar gomman mutane a Darfur — MDD

Faɗan da aka gwabza tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai ya yi sanadiyyar mutuwar gomman mutane a Darfur — MDD

Wani sabon fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai ya yi ɓarna a El-Fasher yayin da fadan ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 27.
Birnin El-Fasher muhimmiyar hanyar rayuwa ce ga miliyoyin mutane a yankin, kuma faɗuwar sa na iya haifar da mummunar yunwa. / Hoto: AA

Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai a farkon wannan mako a muhimmin garin El-Fasher na Darfur, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka kashe akalla mutane 27 a rana guda.

Shaidun gani da ido sun bayar da rahoton cewa, an kai hare-hare ta sama, da harbe-harben bindigogi a birnin tun daga ranar Juma'a, lokacin da aka dauki tsawon sa'o'i ana gwabzawa, inda aka yi ƙiyasin mutum 850 ne suka rasa matsugunansu, a cewar MDD.

Har ila yau, rikicin ya kashe aƙalla mutum 27 a wannan rana, bisa ga abin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce "rahotanni ne da ba a tabbatar da su ba", yayin da birnin ke fama da matsalar rashin sadarwa baki daya, inda likitoci da masu kare hakkin bil'adama suka kasa sanar da duniya labarin.

An ci gaba da gwabza fadan a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, inda suka bayar da rahoton hare-hare ta sama da kuma tashin bama-bamai da suka yi sanadiyyar ƙona gidaje, kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida wa AFP.

A cewar kungiyar agaji ta likitocin Faransa, Doctors Without Borders (MSF), an kashe yara biyu da wani mai kula da su a wani sashin kula da lafiya a ranar Asabar bayan wani harin da sojojin da ke kusa da su suka kai.

Tun a watan Afrilun shekarar da ta gabata ne Sudan ke fama da ƙazamin yaƙi tsakanin sojojin kasar karkashin jagorancin shugaban kasar Abdel Fattah al Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo. .

Rundunar RSF ta ƙwace wasu manyan biranen jihohi hudu cikin biyar a yankin Darfur, yankin da ya kai girman kasar Faransa kuma kusan kashi daya bisa hudu na al'ummar Sudan miliyan 48 ne.

El-Fasher shi ne babban birni na karshe a Darfur wanda baya karkashin ikon kungiyar RSF. Kasashen duniya da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun kwashe makonni suna gargadi game da rikicin da ke shirin kai faruwa a birnin.

An kashe yara a ɗakin kulawa ta musamman

MSF ta fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa wani hari ta sama da sojojin suka kai - ya kai mita 50 (kafa 164) daga Asibitin Yara na Babiker Nahar.

Hakan ya sa rufin ICU ya ruguje, wanda ya yi sanadiyar mutuwar yara biyu da suka rage suna karbar magani a can, da kuma mutuwar a kalla daya mai kula da su,” a cewar wata sanarwa.

"Yaran da aka kashe na cikin wani mawuyacin hali a ICU, amma da an ceci rayukansu," in ji shugaban ayyukan agajin gaggawa na MSF, Michel-Olivier Lacharite.

A duk fadin Sudan, an tilasta wa sama da kashi 70 cikin 100 na asibitoci daina aiki a lokacin yakin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ke kara tabarbarewar tsarin lafiya.

Mayakan sun kai hari kan jami’an kiwon lafiya, inda suka mayar da asibitocin bariki tare da kwasar ganima da kuma hana kayayyakin jinya shiga.

Lacharite ya kara da cewa "Yara 115 ne ke karbar magani a wannan asibiti - yanzu babu kowa," bayan da majinyata da dama suka tsere daga fadan zuwa Asibitin Kudancin El-Fasher da ke kusa, wurin da ya rage a birnin.

Wata majiyar lafiya a asibitin ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa "mutuwarenmu ta cika da gawarwaki" a ranar Juma'a.

MSF ta ce an kai "mutum 160 da suka jikkata - ciki har da mata 31 da yara 19" asibitin, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce "gadaje 100 kawai yake da su."

"A lokacin fadan, asibitin ba shi da motar daukar marasa lafiya da za ta kai mutanen da suka jikkata, kuma tana da karancin kayan aikin jinya da kuma magunguna da ake bukata don jinyar wadanda suka jikkata kuma babu kayan aikin tiyata," in ji MDD a cikin sanarwar ta ranar Lahadi.

TRT World