Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya bayyana a ranar Juma'a cewa kungiyar Tarayyar Turai za ta bai wa kasar Benin kusan Euro miliyan 50 domin tallafawa tsaro da yaki da ta'addanci, ciki har da sayan jirage marasa matuka.
Kasar Benin, tare da maƙwabtanta na gaɓar Tekun Guinea wato Ghana da Togo da Ivory Coast, na fuskantar barazanar tashe-tashen hankula daga masu ikirarin jihadi zuwa arewacinsu a yankin Sahel.
"Muna kan shirin tara Euro miliyan 47 a bana kawai," in ji Michel bayan ganawarsa da shugaban kasar Benin Patrice Talon.
Ya ce za a yi amfani da kudaden ne musamman "don sayan jirage marasa matuka ko ma jiragen tattara bayanan sirri" don "sayen kayan aikin da aka yi nufin amfani da su don tsaro da yaƙi da ta'addanci".
Kwana daya kafin waranr, ya kasance a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast, inda ya kuma tabbatar da aniyar ƙungiyar ta EU ta yaƙi da ta'addanci.
Yankunan arewacin Benin da Togo sun shafe shekaru da dama suna fama da hare-hare da kutse daga mayakan kungiyar IS da kuma Al-Qaeda da ke ci gaba da samun bunkasuwa a yankin Sahel da ke neman komawa kudu.
A baya-bayan nan dai iyakar arewacin kasar da Nijar ta zama abin damuwa tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi a shekarar 2023 da kuma janyewar sojojin Faransa daga yankin Sahel.
Kasar Benin ta aike da dakaru 3,000 zuwa arewacin kasar domin tabbatar da tsaron iyakarta, sannan ta fara daukar karin sabbin sojoji 5,000 a yankin arewacin kasar.
Mahukuntan Benin ba kasafai suke magana kan matsalar tsaro a arewacin kasar ba, amma a watan Afrilun 2023, jami'ai sun ce kasar ta fuskanci kutse kusan 20 daga kan iyaka tun daga shekarar 2021.