Majalisar Tarayyar Turai EU, ta amince da sanya takunkumai kan wasu kamfanoni shida da ake zargin suna da hannu a yakin Sudan, inda dakarun soja na ƙasar (SAF) da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) ke fafatawa tun a watan Afrilun 2023.
A cikin wata sanarwa da Majalisar EU ta fitar a ranar Litinin ta ce kamfanoni shida ne ke da alhakin "tallafa wa ayyukan da ke kawo cikas ga zaman lafiya da sauye-sauyen siyasa a Sudan".
Daga kamfanonin akwai masu hannu wajen ƙera makamai da motoci na rundunar SAF, da Kamfanin Zadna International na Zuba Jari da SAF ke iko da shi da kamfanoni uku da ke da hannu wajen sayen kayan aikin soja na RSF (Al Junaid Multi Activities Co Ltd, Tradive General Trading da kuma kamfanin GSK Advance Ltd).
Majalisar ta ce, "Kamfanonin da aka lissafa suna fuskantar daskarar da ƙadarorinsu. An kuma haramta ba su kudade ko albarkatun tattalin arziki, kai tsaye ko a kaikaice don amfaninsu."
Bala'in jinƙai
Kungiyar EU tana ɗaukar irin matakan da Amurka ta ɗauka ne a watan Yuni, na ƙaƙaba takunkumai kan waɗanda ke ci gaba da ruruta tashe-tashen hankula a Sudan da Birtaniya, inda a shekarar da ta gabata ta ƙaƙaba takunkumai ga 'yan kasuwa masu alaƙa da ƙungiyoyin sojin Sudan.
A watan Nuwamba, EU ta yi Allah wadai da ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankin Darfur na kasar Sudan, tare da yin gargadin hadarin sake samun kisan ƙare dangi bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin shekarar 2003 zuwa 2008 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum kusan 300,000 tare da raba wasu fiye da miliyan biyu da gidajensu.
Zubar da jinin na ci gaba da ta'azzara duk da yunƙurin da kasashen duniya ke yi na samar da tsagaita wuta mai ɗorewa. Yaƙin ya kori mutum sama da miliyan 7.5 daga gidajensu tare da haifar da bala'in jinƙai.
Majalisar ta ce "EU ta damu matuƙa game da halin da ake ciki na jinƙai a Sudan tare da jaddada goyon bayanta ga al'ummar Sudan da kuma ba su haɗin kai."