Ziyarar da ministan tsaron kasar Habasha ya kai Somaliya ita ce ziyarar farko tsakanin ƙasashen ta tun bayan da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi tsami shekara guda da ta wuce. Hoto: Ma'aikatar Harkokin Wajen Habasha/X

Kasashen Habasha da Somaliya sun amince su yi aiki tare a aikin wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka a Somaliya.

Hakan ya biyo bayan ziyarar da ministar tsaron Habasha Injiniya Aisha Mohammed ta kai kasar Somaliya ranar Alhamis.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko tun bayan da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi tsami shekara guda da ta wuce, kan shirin kasar Habasha na gina sansanin sojin ruwa a yankin Somaliya na Somaliland da ya ɓalle.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Habasha ta fitar a ranar Juma'a, "Kasashen biyu sun amince da yin hadin gwiwa kan aikin AUSSOM da karfafa huldar da ke tsakaninsu."

A makon da ya gabata ne Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da izinin wanzar da zaman lafiya da aikin taimakon Tarayyar Afirka a Somaliya - wanda aka fi sani da AUSSOM - don maye gurbin babban aikin yaki da ta'addanci na AU daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.

Ɗaukar matakai

Wakilan kwamitin sulhu 14 daga cikin 15 ne suka kaɗa kuri'ar amincewa da kudurin. Amurka ta ki kada kuri'a.

Kuri'ar ta kara nuna wani mataki na mika ayyukan tsaron kasa ga sojojin kasar Somaliya, in ji majalisar a cikin wata sanarwa.

Ta bai wa mambobin Tarayyar Afirka izinin ɗaukar dukkan matakan da suka dace na tsawon watanni 12, ciki har da tallafa wa gwamnatin Somaliya, wajen rage karsashin ƙungiyoyin Al-Shabaab da Daesh.

A ranar 31 ga watan Disamba ne wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya (ATMIS) ya kare.

Yarjejeniyar Somalia da Ethiopa

Ministan harkokin wajen Masar a ranar Litinin ya bayyana cewa kasarsa za ta shiga cikin sabuwar rundunar wanzar da zaman lafiya a Somaliya.

Kasar Habasha na da dakaru 10,000 a Somaliya domin yakar ‘yan ta’adda na kungiyar al-Shabaab, amma Mogadishu ta yi barazanar korarsu idan Addis Ababa ba ta yi watsi da yarjejeniyar da ta cim ma da yankin Somaliland na Somaliya da ya ɓalle ba.

Yarjejeniyar ta ƙunshi cewa Somaliland ta bayar da bakin ruwanta ga Habasha ta kafa sansanin sojin ruwa da kuma tashar kasuwanci wanda hakan zai sa a samu yiwuwar ta amine da ita a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta

Somaliya dai na daukar Somaliland a matsayin wani yanki na kasarta, kuma babu wata kasa da ta amince da ikirarin yankin na samun 'yancin kai a hukumance.

A watan da ya gabata ne Turkiyya ta kulla yarjejeniyar kawo karshen takaddamar da ta shafe kusan shekara guda ana gwabzawa tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yaba da ci gaban da aka samu a matsayin mai tarihi, kuma tattaunawar ta samu karbuwa daga Tarayyar Afirka, Washington da Brussels.

TRT Afrika da abokan hulda