Zargin kisan kiyashi a Legas a lokacin zanga-zangar ya jawo ce-ce-ku-ce matuka a Nijeriya. Hoto/Reuters

Gwamnatin Legas da ke Kudancin Nijeriya ta yi karin haske kan wasu labarai da ta ce na bogi ne da ake yadawa cewa za ta binne mutum 103 da aka kashe a Lekki Toll Gate a lokacin zanga-zangar Endsars ta 2020.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, gwamnatin ta musanta wannan batun inda ta ce mutum 103 da aka rubuta a takardar an gano su ne a sassa daban-daban na Legas.

Labarin binne dimbin mutanen ya fito ne sakamakon wata takarda da aka gani a ranar Lahadi inda kafafen watsa labarai suke ikirarin cewa watakila mutanen su ne wadanda jami’an tsaro suka kashe a Lekki Toll Gate.

Tuni dama adadin mutanen da suka rasu a zanga-zangar, wadda aka yi a Oktobar 2020, ya zama wani abin da ake jayayya a kai. Adadin baya-bayan nan ya fi wanda aka bayar da rahoto a baya.

Zanga-zangar ta girgiza kasar inda ta sa aka yi sauyi a aikin dan sanda. Masu fafutika sun zargi jami’an tsaro da bude wuta kan masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate da ke Legas inda ake zarginsu da kashe mutane da dama.

A Disambar 2021, gwamnatin Legas ta musanta cewa jami’an tsaro sun yi wa masu zanga-zanga da ba sa dauke da makamai “kisan kiyashi”, inda ta ce mutum daya ne kawai harbin bindiga ya sama a lokacin zanga-zangar.

Watsi da zargi

Sai dai a sanarwar da gwamnatin Legasa ta fitar ta ce wadanda za a binne ba a Lekki Toll Gate aka kashe su ba.

Gawarwaki ne da aka gano a sassa daban-daban na birnin sakamakon rikici, “ba daga Lekki Toll Gate ba kamar yadda aka rinka yadawa,” in ji gwamnatin.

“A bayyane take cewa rikicin Endsars na 2020 wanda ya rikide zuwa tarzoma a sassa daban-daban na Legas ya sa an samu mutane da dama wadanda suka rasa ransu a jihar,” in ji Dakta Olusegun Ogboye, babban sakatare a ma’aikatar ilimi a wata sanarwa.

“Ma’aikatar kula da lafiyar muhalli ta Legas (SEHMU) ta dauki gawarwakin da aka kashe bayan rikicin Endsars a Fagba da Ketu da Ikorodu da Orile da Ajegunle da Abule-Egba da Ikeja da Ojota da Ekoro da Ogba da Isoli da Ajah, har da na fasa fursuna a gidan yarin Ikoyi,” in ji shi.

Gawarwakin da ba a san masu su ba

“Gawarwaki 103 da aka sanar a wannan takardar an same su ne daga wannan lamari ba da daga Lekki Toll-gate ba kamar yadda ake zargi. Domin guje wa shakka, babu wata gawa da aka dauko daga Lekki Toll Gate,” in ji Ogboye.

Babu tabbaci kan lokacin da za a binne gawarwakin sai dai wasu ‘yan Nijeriya na ta yin tambayoyi kan dalilin da ya sa aka dauki lokaci mai tsawo ba a binne gawarwakin ba. Hukumomi sun mayar da martani inda suke cewa “bayan kusan shekara uku ba a samu masu gawarwakin ba, inda wurin ajiye gawarwaki ke kara cika.

Wannan ne ya ja za a rage gawarwakin dakin ajiyar gawarkin, wanda wata hanya ce da ake bi a hankali da sharuda na kiwon lafiya da shari’a saboda ana iya samun dangin mamaci ya zo ya ga gawar dan uwansa bayan shekaru.

TRT Afrika