Kwamitin bincike na majalisar dokokin jihar Kaduna ya ya kamata a binciki almundahar kudaden da ake zargin gwamnatin El-Rufai da yi. /Hoto Nasir El Rufa'i

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna da ke Nijeriya Nasiru El-Rufai ya yi watsi da batun bincike kan gwamnatin da ya yi ta tsawon shekara takwas tsakanin 2015 da 2023 da kwamitin wucin gadi na majalisar dokoki ya bayar da umarnin a yi, inda ya ce siyasa ce tsagwaronta tattare da batun.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ta hannun kakakinsa, Muyiwa Adekeye, tsohon gwamnan jihar ta Kaduna ya bayyana cewa ya jagoranci jihar da nagarta da ƙwarewa a tsawon shekara takwas.

A ranar Laraba ne kwamitin da majalisar dokoki ta kafa kan binciken dukkan ta'ammali da kudade, ciyo bashi da bayar da kwangila na gwamnatin El-Rufai ya miƙa rahotonsa ga zauren majalisar.

Shugaban kwamitin binciken na wucin gadi, Henry Zacharia ya ce mafi yawan bashin da aka karɓo a lokacin mulkin El-Rufai ba a yi amfani da shi a ɓangaren da ya kamata ba, a wasu lokutan kuma ba a bi hanyar da ta dace ba wajen karɓar bashin.

Shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Liman ya bayyana cewar ana zargin gwamnatin El-Rufai da sace Naira biliyan N423, inda suka bar jihar da ɗimbin bashi.

Sakamakon haka kwamitin ya bayar da shawarar jami'an tsaro da na yaƙi da almundahana su binciki El-Rufai da muƙarrabansa tare da gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin amfani da muƙamansu ta mummunar hanya da sace kuɗin gwamnati.

Kwamitin ya kuma bayar da shawarar dakatar da Kwamishinan Kuɗi na jihar Kaduna Shizer Badda nan-take, wanda ya riƙe irin wannan matsayi a lokacin gwamnatin El-Rufai.

Da yake mayar da martani, kakakin El-Rufai Adeyeke ya sake jaddada nagartar tsohon gwamnan inda ya yi watsi da wannan zargi da ya bayyana a matsayin abin kunya.

Ya ce "Malama Nasir El-Rufai na alfahari sosai da nasarar da ya samu a lokacin mulkinsa da irin ayyukan da ya yi a jihar Kaduna. Babu wani yunƙuri na ɓata suna da majalisar jiha ke yi da zai iya kawar da wannan ƙwazo da nasara a aikin gwamnati da rayuwar gwamnan."

Adeyeke ya ci gaba da cewa "Malam Nasir El-Rufai na tabbatarwa da 'yan Nijeriya masu kaifin hankali cewa ya hidimta wa jihar Kaduna da nagarta da dukkan iyawarsa, tare da samun taimakon jajirtattun abokan aiki. Ya kamata a yi watsi da wannan binciken mai tattare da siyasa zalla."

TRT Afrika