Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai na cikin mutum uku da Majalisar Dattawan Nijeriya ba ta tabbatar wa mukaman minista ba.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman da ta yi ranar Litinin a yayin da suka tabbatar wa mutum 45 da mukaman minista.
Sauran mutanen da ba a tabbatar wa mukaman ba su ne tsohon gwamnan riko na jihar Taraba Sani Danladi da kuma Stella Okotete.
Majalisar dattawan ta bukaci a kara binciken sirri a kansu.
Da ma dai a lokacin da ya je gaban majalisar domin a tantance shi, Nasir El-Rufai ya fuskanci tambayoyi daga wurin wani dan majalisar dattawa da ya ce an aika masa wasikar korafi a kan tsohon gwamnan na jihar Kaduna game da kalamansa kan tsaro da hadin kan Nijeriya.
Ga jerin mutanen da Majalisar Dattawan ta tabbatar wa mukaman ministoci:
1. Abubakar Kyari (Jihar Borno)
2. Abubakar Momoh (Jihar Edo )
3. Nyesom Wike (Jihar Ribas)
4. Joseph Utsev (Jihar Binuwai)
5. John Eno (Jihar Cross River )
6. Bello Mohamed (Jihar Sokoto)
7. Mohammed Badaru Abubakar (Jihar Jigawa)
8. Yusuf Maitama Tuggar (Jihar Bauchi)
9. Uju Ken Ohaneye (Jihar Anambra)
10. Olubunmi Tunji Ojo (Jihar Ondo)
11. Nkeiruka Onyejeocha (Jihar Abia)
12. Betta Edu (Jihar Cross River)
13. Imaan Suleiman (Jihar Nasarawa)
14. David Umahi (Jihar Ebonyi)
15. Adebayo Olawale Edun (Jihar Ogun)
16. Ahmed Musa Dangiwa (Jihar Katsina)
17. Uche Nnaji (Jihar Enugu)
18. Dele Alake (Jihar Ekiti)
19. Waheed Adebayo Adelabu (Jihar Oyo)
20. Muhammad Idris (Jihar Neja)
21. Ali Pate (Jihar Bauchi)
22. Doris Uzoka (Jihar Imo)
23. Lateef Fagbemi (Jihar Kwara)
24. Ekperikpe Ekpo (Jihar Akwa)
25. Hannatu Musawa (Jihar Katsina)
26. Ibrahim Geidam (Jihar Yobe)
27. Aliyu Sabi Abdullahi (Jihar Neja)
28. Heineken Lokpobiri (Jihar Bayelsa)
29. Alkali Ahmed Sa’eed (Jihar Gombe)
30. Yusuf Tanko Sununu (Jihar Kebbi)
31. Atiku Bagudu (Jihar Kebbi)
32. Bello Matawalle (Jihar Zamfara)
33. Adegboyega Oyetola (Jihar Osun)
34. Simon Bako Lalong (Jihar Filato)
35. Abdullahi Tijjani Gwarzo (Jihar Kano)
36. Bosun Tijjani (Jihar Ogun)
37. Mariya Mahmoud (Jihar Kano)
38. Isiyaka Salako (Jihar Ogun)
39. Tunji Alausa (Jihar Legas)
40. Lola Ade John (Jihar Legas)
41. Tahir Mamman (Jihar Adamawa)
42. Zephaniah Jissalo (Babban Birnin Tarayya)
43. Uba Maigari Ahmadu (Jihar Taraba)
44. Shuaibu Abubakar Audu (Jihar Kogi )
45. Festus Keyamo (Jihar Delta )