Mai alfarma Sarkin Musulman Nijeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya ce an ga watan Shawwal a kasar.
Ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Sokoto ranar Alhamis.
Ya ce gobe Juma'a ta kama daya ga watan Shawwal wadda ta yi daidai da 21 ga watan Afrilun 2023.
Sarkin Musulmin ya ce an ga watan ne a sassa daban-daban na Nijeriya.
Ya yi kira ga Musulmai su yi riko da kyawawan halaye da suka koya lokacin azumin watan Ramadan yana mai yin addu'ar samun zaman lafiya a kasar.
Ya roke su da su cigaba da zama cikin zaman lafiya da mutunta juna.
Kazalika an ga watan Sallah a Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Nijeriya.
Tun da farko, hukumomi a Saudiyya sun ce an ga sabon wata a kasar don haka gobe Juma'a za ta kasance daya ga watan Shawwal.
Hukumomin sun bayyana ganin watan ne a shafin Twitter na Haramain mai kula da Masallatai masu tsarki.
Ita ma kasar Turkiyya gobe za a yi karamar Sallah.
An ga watan ne bayan Musulmai sun kwashe kwana 29 suna azumin watan Ramadan.
Azumin watan Ramadan na daya daga shika-shikan Musulunci.