EFCC ta gurfanar da mutumin da ya zambaci matar Sarkin Bichi naira miliyan 20

EFCC ta gurfanar da mutumin da ya zambaci matar Sarkin Bichi naira miliyan 20

Sanarwar ta kara da cewa bayan ya karbi kudin ne, mutumin da ake zargi sai ya karkatar da kudin zuwa amfanin kansa.
Hukumar EFCC ce take yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa:Hoto/Facebook/EFCC

Hukumar da ke Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Kasa (EFCC) ta ce ta gurfanar da wani mutum mai suna Umar Bello Sadiq a gaban wata babbar kotu a jihar Kano bisa wasu tuhume-tuhume uku.

Hukumar ta ce tuhume-tuhumen sun hada da karkatar da kudi da bayar da cek din bogi.

Kazalika ta ce ta gabatar da mutumin a gaban kuliya ne tare da kamfaninsa mai suna Marula Global Links, bayan ya karbi naira miliyan 20 daga hannun Faridah Nasir Bayero, wato matar Sarkin Bichi Nasir Ado Bayero da sunan za a zuba jari a harkar hakar ma'adanai, kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na X wanda a baya ake kira Twitter.

Sanarwar ta kara da cewa bayan ya karbi kudin ne sai ya karkatar da su zuwa amfanin kansa.

Sai dai ya musanta zarge-zargen yayin da aka karanta masa su.

Bayan haka ne lauya mai gabatar da kara Sadiq Kurawa ya bukaci kotun ta sanya ranar fara shari'ar yayin da lauyan wanda ake kara Shuaibu Muazu ya bukaci kotu ta bayar da belin mutumin da ake tuhuma.

Mai Shari'a Zuwaira Yusuf ta bayar da belin wanda ake zargi kan Naira 500,000 da mutum biyu da za su tsaya masa wadanda wajibi ne su kasance danginsa na jini, a cewar sanarwar.

A karshe kotun ta dage zamanta har zuwa ranar 24 ga watan Nuwamban bana don fara shari'ar.

TRT Afrika