Kazalika binciken EFCC ya gano cewa Aisha da mijinta Abubakar (wanda har yanzu bai zo hannu ba), sun karkatar da kuɗaɗen zuwa asusun bankuna daban-daban. Photo: Reuters

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa EFCC ta gurfanar da wasu mata da miji a gaban kotu inda aka tuhumarsu bisa kan laifuka biyar da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗade har N410,518,000.

An gurfanar da ma’auratan Aisha Salihu Malkohi da aka fi sani da Ummitah Arab Money da mijinta Abubakar Abubakar Sadiq Mahmoud ne a gaban wata babbar kotu a Jihar Kano ranar Juma’ar da ta gabata.

Ana zargin su da karbar kudi har naira 225,259,000 na wata Farida Ibrahim daga watan Janairu har zuwan Disamban 2022 da nufin za su sayo mata motoci 64 daga Saudiyya, kamar yadda sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin ta fada.

“Kun karbi kudaden duk da cewa kun san ƙarya ne, don haka kun aikata laifi a karkashin dokar laifukan da suka shafi zamba ta 2006,” kamar yadda takardar tuhumar ta ce.

Wacce ake zargin dai ta amsa dukkan laifuka biyar din da aka karanta mata, inda nan da nan lauyan EFCC Zarami Mohammed ya nemi kotu da ta sanya ranar yanke hukunci.

Sai dai lauyan ma’auratan ya nemi a ba da belinsu amma hakan bai samu ba.

Kotu ta bai wa EFCC izinin ci gaba da riƙe su har sai zama na gaba da za a yi ranar 15 ga watan Disamban 2023.

EFCC ta kama Aisha ne bayan da wasu mutum biyu Farida Ibrahim da Ibrahim Mohammed Abdulrahman suka shigar da ƙorafi a gabanta suna zargin Aisha da haɗa baki da mijinta wajen zambatar su, da nufin za su sayo musu motoci da gwala-gwaldai da kayan lantarki da kayan kicin daga Saudiyya.

“Karbar korafin ke da wuya sai hukumar EFCC ta ƙaddamar da bincike wanda ya gano cewa Aisha ta karbi kudi har naira miliyan ɗari huɗu da goma da dubu ɗari biyar da goma sha takwas, N410,518,000 ta asusun bankunan kamfaninta, Golden Grass Hill International Ltd da asusun mijinta na banki.

Kazalika binciken EFCC ya gano cewa Aisha da mijinta Abubakar (wanda har yanzu bai zo hannu ba), sun karkatar da kuɗaɗen zuwa asusun bankuna daban-daban.

TRT Afrika