EFCC ta ce an ja hankalinta ne kan yadda masu shirya wasannin barkwanci da fina-finai suke amfani da kaya mai dauke da tambarin hukumar ba tare da izini ba/Hoto: EFCC

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta EFCC ta gargadi masu wasan kwaikwayo su guji amfani da irin kayanta wurin wasan barkwancinsu.

A wata sanarwa da kakakinta Wilson Uwajeren ya fitar ranar Litinin, EFCC ta ce an ja hankalinta ne kan yadda masu wasannin barkwanci da fina-finai suke amfani da kaya mai dauke da tambarin hukumar ba tare da neman izini ba.

“EFCC na son sanar da jama’a cewa bai halatta a dinga amfani da kaya mai tambarinta wajen yin fina-finai ba tare da izini ba.

“A yayin da hukumar ke jin dadin yadda wasu ke son shirya fina-finai masu dauke da sakonnin aikin da take ke yi don wayar da kan jama’a, dole sai an fara neman izininta tare da nuna mata fitowar da za a yi da sunanta a fina-finai don ta tabbatar babu wani sako da ya saba da irin ayyukanta,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce sashen hulda da jama’a na EFCC yana da kwarewar da zai iya aiki da masu shirya fina-finai da ke da burin hada gwiwa da hukumar wajen shirya fim ko wasannin barkwanci da nufin ilimintar da mutane, musamman matasa kan munin cin hanci da rashawa.

A karshe hukumar ta ce duk wanda aka kama da laifin yin gaban kansa wajen shirya fim ko barkwanci ba tare da izinin EFCC din ba, to za a dauki mataki a kansa.

TRT Afrika