ECOWAS ta karyata ce wa tana so sojojin Nijar su mika wa farar-hula mulki nan da wata tara

ECOWAS ta karyata ce wa tana so sojojin Nijar su mika wa farar-hula mulki nan da wata tara

“Rahoton, wanda aka yi shi da Faransaci... na karya ne, kuma ya kamata a dauke shi a matsayin labarin karya," in ji ECOWAS.
“Rahoton, wanda aka yi shi da Faransaci... na karya ne, kuma ya kamata a dauke shi a matsayin labarin karya," in ji ECOWAS.  Hoto: AP

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta karyata rahotannin da ke cewa shugaban kungiyar, Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban Nijaeriya, ya nemi sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su mika mulki nan da wata tara.

“An jawo hankalin Kungiyar ECOWAS a kan wani rahoto da ke cewa kungiyar ta nemi sojojin Nijar su bi wani wa'adi na mika mulki," a cewar ECOWAS a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, wato Twitter a baya da kuma shafinta na Facebook.

“Rahoton, wanda aka yi shi da Faransaci... na karya ne, kuma ya kamata a dauke shi a matsayin labarin karya."

ECOWAS tana kan matsayarta ta cewa bukatarta ga sojojin Nijar a bayyane take.

“Dole ne hukumomin sojin Nijar su mayar da doka da oda ba tare da bata lokaci ba ta hanyar mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulkinsa,” a cewar ECOWAS.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun katse lantarki da ruwa a ofishin jakadancin Faransa

Kalaman da aka ce Tinubun ya fada tun farko a ranar Alhamis su ne cewa gwamnatin mulkin sojin Nijeriya a shekarar 1999 a karkashin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar ta mika mulki ga hukumomin farar hula kasa da shekara da hawansa.

A don haka ne rahoton farkon ya ce Tinubu ya nemi gwamntin sojojin juyin mulkin na Nijar karkashin jagorancin Abdourahamane Tiani da su bi sahun Janar Abdulsalam.

“Shugaban kasar Nijeriyar bai ga wani dalili da zai hana a bi irin wannan salon ba a Nijar, idan har hukumomin mulkin sojin suna son gaskiya," kamar yadda AFP ta ruwaito, tana mai ambato wata sanarwa daga ofsihin Tinubun.

A ranar 26 ga watan Yuki ne wani juyin mulkin sojoji ya hambarar da Bazoum daga mulki. Sojojin juyin mulkin sun zarge shi da gaza magance talaucin da ake fama da shi a kasar.

TRT Afrika