Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce ƙofar ƙasashe mambobinta a buɗe take domin shige da ficen ‘ya’yan ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar da suka fice daga cikinta.
A wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba a shafinta na X, ECOWAS ta ce duk da cewar daga ranar Laraba 29 ga watan Janairun shekarar 2025 ne ficewar ƙasashen daga ECOWAS ta tabbata, tana kira ga ƙasashe mambobinta su saurara wa ‘ya'yan ƙasashen.
Sanarwar ta ce saboda haɗin kai na yankin da amfanin jama’a da kuma shawara da muhukuntan ECOWAS suka yanke ta barin ƙofar ƙungiyar a buɗe, ECOWAS za ta ci gaba da amincewa da fasfo ɗin ‘ya’yan ƙasashen da ke ɗauke da tambarin ECOWAS.
Ta ƙara da cewa ta nemi dukkan ƙasashen ECOWAS su ci gaba da bin tsarin sassaucin kasuwanci bisa shige da fice na kayayyaki da ma’aikata daga ƙasashen AES zuwa ƙasashen ECOWAS.
ECOWAS ta kuma nemi mambobinta su ci gaba da bai wa ‘ya’yan ƙasashen 'yancin shiga da ficewa da kuma ayyuka a ƙasashen ECOWAS ba tare da neman biza ba.
Kazalika ECOWAS ta nemi ƙasashen su ba da haɗin kai ga jami’an ECOWAS daga ƙasashen uku a ciki aikin su ga ECOWAS.
Ta ce ƙungiyar za ta ci gaba da yin hakan ne har zuwa lokacin da shugabannin ƙasashen ECOWAS za su yanke shawara game da irin hulɗar da za su yi da ƙasashen uku.
Tarihi mai cike da ce-ce-ku-ce
A bara ne dai ƙasashen uku suka yi shelar ficewa daga ƙungiyar ECOWAS bayan ce-ce-ku-ce tsakanin ECOWAS da ƙasashen sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a cikinsu.
ECOWAS dai ta dakatar da ƙasashen ne bayan juyin mulki kana ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi tare da barazanar amfani da ƙarfin soji don mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki.
Wannan ne ya sa ƙasashen Mali da burkina Faso suka ce za su haɗa kai wajen yaƙar duk wata ƙasar da ta yaƙi Nijar.
Bayan hakan ne dai shugabannin ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar suka kafa ƙungiyar AES tare da yin shelar ficewa daga ECOWAS