Jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya sun sake kama tsohon shugaban Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele bayan da suka kai ruwa rana da jami'an Hukumar Gidan Yari kan batun cigaba da tsare shi sakamakon belinsa da kotu ta bayar.
A ranar Talata ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas ta bayar da belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele wanda Shugaba Bola Tinubu ya dakatar.
Mai shari’a Nicholas Oweibo ne ya bayar da belin kan naira miliyan 20 da kuma bayar da mutum guda wanda zai tsaya masa, bayan yin watsi da ikirarin gwamnatin tarayya cewa za iya guduwa.
Sai dai alkalin kotun ya ba da umarnin a kai Emefiele gidan yari har sai ya cika sharuddan belin tukunna.
Kai ruwa rana
Bayan tashi daga shari'ar an ga shugaban CBN din da aka dakatar zagaye da lauyoyinsa a dakin shari'ar.
Su kuwa jami'an DSS wadanda dama su suka kai Emefiele kotun, sai suka ajiye motarsu kirar Hilux da nufin sake tafiya da shi don cigaba da tsare shi a hannunsu, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
Wannan lamari ya sa babban lauyan da ke kare Emefiele da sauran lauyoyinsa suka ankarar da abin da ke faruwa na sake tsare wanda suke karewa da DSS ke son yi.
Hakan ya sa jami'an gidan yarin su ma suka fara fafutukar daukarsa bisa umarnin da kotu ta yi na cewa su za su tafi da shi, har hakan ya jawo aka kai ruwa rana tsakanin su da jami'an DSS.
Ganin hakan ne ya sa dole lauyoyin Emefiele suka hakura tare da barin DSS su dauke shi "don gudun musayar wuta", kamar yadda suka ce.
A karshen jami'an gidan yarin sun bar kotun inda na DSS suka sake daukar Emefiele.
Tuhume-tuhume
A ranar Talata ne tsohon Mista Emefiele ya hallara a gaban Kotun Tarayya da ke zamanta a Ikoyi da ke Legas ranar Talata.
Ana tuhumar Emefiele da zarge-zarge biyu da suka hada da mallakar bindiga da kuma harsasai ba bisa ka’ida ba.
Tun da fari gidan talabijin na Channels a Nijeriya ya wallafa wani bidiyo wanda ya nuna yadda jami’an na DSS suka fito da Mista Emefiele daga wata farar mota kirar Toyota Hilux inda aka shige da shi cikin kotun.
Alkali Nicholas Oweibo ne ya saurari karar ta Mista Emefiele a Babbar Kotun da ke Ikoyi a Legas.
An kama Emefiele tun a ranar 9 ga watan Yunin 2023 inda hukumar DSS ta ci gaba da tsare shi.
Sai dai daga baya wani umarnin kotu ya bukaci hukumar ta DSS da ta gurfanar da Mista Emefiele gaban kotu ko kuma ta sake shi.
Jim kadan bayan haka ne DSS din ta shigar da kara a gaban kotu kan zarge-zarge biyu da suka hada da samunsa da bindiga mai baki daya wadda ba ta da lasisi.
Haka kuma ana zarginsa da mallakar harsasai 123 wadanda hukumar DSS ta ce ta gani a gidansa da ke Maitama Abuja.