Wani soja daga ƙungiyar M23 na leƙawa ta wani abin hangen nesa da aka gano daga cikin kayayyakin da sojoji suka tsere suka bari a tashar ruwa ta Goma. / Hoto: AFP

Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ta bukaci kasar Chadi da ta ba ta tallafin soji domin taimakawa wajen yakar 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda a yankunan gabashin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wata majiya daga fadar shugaban Kongo.

Ministan hadin kan yankin na DRC ya gana da shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno a ranar Talata a madadin shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi, kamar yadda fadar shugaban kasar Chadi ta bayyana a wani sako da ta wallafa a shafin Facebook.

Ba a bayyana cikakkun bayanai kan tattaunawar ba. Wani jami'in Chadi da ke da masaniya kan tattaunawar ya ce Chadi na duba yiwuwar neman tallafi daga DRC, amma har yanzu ba ta yanke shawara kan bukatar ba.

Wata majiya a fadar shugaban kasar Kongo a ranar Laraba ta shaida cewa Kinshasa ta bukaci tallafin soji da diflomasiyya daga kasar Chadi.

Sai dai babu wata majiya da ta bayar da ƙarin bayani. Sun ƙi a bayyana sunansu saboda dalilai na sirri.

Mai magana da yawun gwamnatin Chadi Gassim Cherif bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba a ranar Laraba.

Haka ita ma mai magana da yawun Tshisekedi, Tina Salama, ta ce ba ta da wani bayani kan lamarin.

Ba a tattauna batun tallafin a hukumance ba, amma "ba za a iya kore wani abu a cikin zancen ba," in ji wani jami'in Chadi.

A makon da ya gabata, Ministan Harkokin Wajen Chadi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa aikewa da tallafin soji zuwa DRC "jita-nita ce kawai".

TRT World