Daga Charles Mgbolu
Garin Badagry mai cike da tarihi a Legas, wato cibiyar kasuwancin Nijeriya, ya karbi bakuncin bikin karo na hudu mai suna 'Door of Return', wato wani biki wanda 'yan Afirka da ke zaune a kasashen waje ake tarbar su ta hanyar da aka fitar da iyaye da kakanninsu daga Afirka a matsayin bayi zuwa kasashen Yammacin Duniya.
Taron kwana ukun wanda aka fara daga ranar 19 zuwa 21 ga Oktoba ana fara shi ne da isowar 'yan Afirka mazauna ketare a kwale-kwale a wani salo na kwaikwayon dawowar kakanninsu wadanda aka tafi da su lokacin cinikin bayi daruruwan shekaru da suka wuce.
Kayan da aka rina da launukan Afirka, bakin da suka zo daga ketare sun yi tafiyar kilo mita 1.5 a hanyar da ake wucewa da bayi zuwa teku.
'Yan Nijeriya sun yi bikin hatta a kafafen sada zumunta.''Kodayake abu ne mai wuya," in ji Julius Garvey wani da ke zaune a ketare kuma mahaifinsa dan kishin Afirka ne wanda aka haifa a Jamaica.
Marcus Garvey ya ce yayin da yake magana kan wahalar da ke tilasta wa 'yan Afirka zama bayi.
An yi jigilar tsakanin 'yan Afirka miliyan 10 zuwa miliyan 28 a tekun Atlantic tsakanin karni na 15 zuwa karni na 19 a matsayin bayi a yankin Amurka da Caribbean.
Da yawa daga ciki sun ce abin da ya faru a kofar Door of Return yana tuna ta'asar da aka yi wa Afirka yayin cinikin bayi.
"Ina so na fahimci wahalar da kakanninmu suka shiga da kuma abubuwan da suka faru da su, saboda suna da muhimmanci," in ji Rgarge Romero wani dan Spain dan asalin Afirka wanda ya halarci bikin.Bayan tafiyar mai nisa, an yi musu maraba da abubuwan sha ta kafar 'Door of Return'.
"Wani abu ne da ke tuna musu da baya – ta fuskar tattalin arziki da tunanin da sauransu. Suna so su ga abin da za su yi a nahiyar misali ta hanyar gina wata fada a nan Badagry.
Saboda haka batu ne na zuba jari a nahiyar," in ji Abike Dabiri Shugabar Hukumar da ke Kula da Nijeriya da ke Zaune a Ketare.