Hukumar da ke shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a ta Nijeriya, JAMB, ta ce ta bai wa dukkan cibiyoyinta umarnin kama duk wasu iyaye da aka gani a ko da kusa da wuraren da za a yi jarrabawar ta UTME ta shekarar 2024.
An ba da umarnin ne a wajen taron ƙarshe da hukumar ta yi da masu cibiyoyin da za a yi jarrabawar a cikinsu, wanda aka yi ta intanet a jiya Laraba.
“Wannan umarnin ya zama dole ne biyo bayan kutsen da wasu iyaye suka yi a lokutan jarrabawowin da hukumar ta yi a baya,” kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin ta faɗa.
Ya ƙara da cewa shugaban JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce duk wasu iyaye da suka saɓa wa umarnin nan, ba kama su kawai za a yi ba, za a kuma haramta wa ƴaƴansu rubuta jarrabawar.
“Wannan matakin ya zama dole domin an gano cewa da yawa daga cikin wadannan iyayen da ke kutsawa suna taimakawa wajen yin satar amsar jarrabawa, yayin da wasu kuma ta hanyar ayyukansu sun kawo cikas ga jarrabawar hukumar a baya.
“Wasu ɓata gari kuma suna ɓad-da-kama a matsayin iyaye don kutsawa cikin cibiyoyin jarrabawar su yi abubuwan da ba su dace ba.”
Don haka, Farfesa Oloyede ya bayyana cewa hukumar ta umurci jami’an tsaro da su yi aiki da cibiyoyin domin kamo duk wasu iyaye da ke da hannu a ciki, da suka zo kusa da cibiyoyin.
Take dokokin rubuta JAMB
Shugaban hukumar ya ce bisa ga tsayayyun manufofin ƙasa kan ilimi, dole mai son rubuta jarrabawar ya kai shekara 17.
“Don haka a bayyane yake cewa wadannan iyayen ba sa bari ƴaƴnsu su kammala ajujuwan da suka kamata kamar yadda doka ta tsara, don haka suke bin ƴaƴan nasu har wajen jarrabawar da nufin taimaka musu.”
JAMB ta ce hakan ne ya sa ya kamata a hukunta iyayen saboda a baya sun sha cusa yaran da shekaransu ba su kai ba don su zana jarrabawar ba bisa ƙai’da ba.
Hukumar ta kuma yi amfani da damar da taron ya bayar na shawartar ɗalibai da su kiyaye bayanansu na sirri, da adireshin imel, da kuma rajista da lambobin wayarsu.
An ba da wannan shawarar ce saboda wasu ɗaliban, waɗanda za a iya yaudarar su don amfani da shafukan intanet na bogi.
Don haka, Hukumar ta sanar da ɗalibai cewa idan aka gano bayanansu na sirri a ɗaya daga cikin irin wadannan shafuka, za a dauke su a matsayin masu laifi kuma a gurfanar da su a gaban ƙuliya.
Gargaɗin ɗalibai
Kazalika, shugaban na JAMB ya ce an kammala dukkan shirye-shirye na zana jarrabawar UTME ɗin ta 2024, kuma za a yi a cibiyoyi 700 a faɗin ƙasar.
Ya bayyana cewa hukumar na sa ran za a gudanar da jarrabawar ba tare da wata matsala ba amma duk da haka ta yi tanadin isasshiyar hanyar magance duk wata matsala ta fasaha da ka iya faruwa a yayin jarrabawar.
Sai dai ya yi gargadin cewa idan aka samu matsala a wani zango na jarrabawar, za a bar ɗaliban zango na gaba su yi tasu jarrabawar, yayin da waɗanda suka fuskanci matsalar kuma za a sake saka musu wani lokacin na yin ta.
Don haka hukumar ta ja hankalin ɗailbai da ka da su tada hankalinsu idan aka samu matsala. "Kuma idan har wani ɗalibai ko iyaye suka kawo cikas ga duk wani zama da zai biyo baya, saboda matsalar da aka samu a zaman farko, to za a hana ɗalibin yin jarrabawar.
Sannan kuma Farfesa Oloyede ya roƙi masu cibiyoyin da za a yi jarrabawar da su ɗauki hakana matsayin aikin yi wa ƙasa hidima ba kasuwanci don riba ba.
Kuma ya roƙe su da su tona asirin baragurbin cikinsu.