Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta yi ƙarin haske dangane da kama ɗan jaridar nan mai binciken ƙwaƙwaf na gidan jaridar FIJ wanda ta tsare tsawon kwanaki 10.
A sanarwar da rundunar ƴan sandan ta fitar ta bayyana cewa ta bi doka wurin tsare Mista Daniel Ojukwu.
Tun da farko ƴan sandan sun kama Mista Ojukwu ne kan zargin saɓa dokar yaƙi da laifuka na intanet
An kama dan jaridar tare da mayar da shi babban birnin Nijeriya Abuja biyo bayan rahotonsa game da almundahanar kudi sama da Naira miliyan 147 ($104,600) da yake zargin wani babban jami'in gwamnati da aikatawa.
Bayan an kama shi, an samu kiraye-kiraye daga abokan aikinsa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran ƙungiyoyi wanda hakan ya jawo aka sake shi a ranar Juma’a.
Rundunar ‘yan sandan ta ce zarge-zargen da ake yi wa Ojukwu ya samo asali ne daga rahoton da ya shafi hada-hadar kudi wanda hakan ya ja aka gudanar da bincike.
A sanarwar, rundunar ƴan sandan ta ce ba ta taɓa hana bayar da belin Ojukwu ba, domin ta tanadi cewa sai ya cika sharuɗan belin.
Sai dai ta ce ta sake shi a ranar Juma’a 10 ga watan Mayu bayan cika sharuɗan beli, kafin a soma shari’arsa a Babbar Kotun Tarayya.
Ƴan sandan sun jaddada cewa sakin da aka yi wa Ojukwu ba shi da alaƙa da zanga-zangar da aka gudanar a hedikwatar ƴan sanda a ranar 9 ga watan Mayu, sai dai sakamakon ya cika sharuɗan beli.