Fitaccen mai kudin nan na Nijeriya Aliko Dangote ya koma matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, kasa da mako guda bayan mai kudin nan na Afirka ta Kudu Johann Rupert ya doke shi, kamar yadda mujallar Forbes ta tabbatar.
A halin yanzu arzikin Dangote ya kai dala biliyan 10.5, kamar yadda wani jerin mutanen da suka fi arziki a duniya ya nuna. Ya sauka daga matakin tun a farko bayan ya samu raguwa da dala biliyan 3.8.
Dangote a baya ya rike kambin wanda ya fi kowa kudi a Afirka na sama da shekara 10. Shi ne mai hannun jari mafi tsoka a kamfanin simintin Dangote.
Fitaccen mai arzikin ya bude matatar mai mafi girma a Afirka a watan Mayun 2023 wadda za ta iya tace ganga 650,000 a kullum.
Tun daga 1987 Forbes ke bibiyar shahararrun masu biliyoyin kudi na duniya.
Ga jerin mutum goma wadanda suka fi kudi a Afirka:
- Aliko Dangote - Nijeriya, $10.5 billion
- Johann Rupert da iyalai - Afirka ta Kudu, $10 billion
- Nicky Oppenheimer da iyalai - Afirka ta Kudu, $8.3 billion
- Nassef Sawiris - Masar, $7.2 billion
- Abdulsamad Rabiu - Niijeriya, $6.3 billion
- Nathan Kirsh - Eswatini, $5.9 billion
- Issad Rebrab da iyalai - Algeria, $4.6 billion
- Mohamed Mansour - Masar, $3.6 billion
- Naguib Sawiris - Masar, $3.3 billion
- Mike Adenuga - Nijeriya, $3.2 billion