Wata babbar kotu a Ghana ta yanke wa wani dan Nijeriya hukuncin zaman gidan yari na shekara goma tare da horo mai tsanani.
An yanke masa hukuncin ne bayan an same shi da miyagun kwayoyi.
A ranar 11 ga watan Disamba ne hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar Ghana ta kama Ernest Nnajuiba Ukechukwu da hodar ibilis da nauyinta ya kai gram 16568.83.
An kama shi a filin jirgin sama na Kotoka da ke Accra Daga inda a nan ne ma’aikatan hukumar suka kama shi inda daga baya suka gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin shiga da miyagun kwayoyi a cikin kasar.
Mista Ernest asalinsa dan Nijeriya ne kuma mazaunin kasar Brazil.
Hukumar da ke yaki da miyagun kwayoyin ta sha kama miyagun kwayoyi a filin jirgin na Kotoka.
Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta kama dauri 54 na ganyen tabar wiwi da nauyinsu ya kai kilo 12.67 a filin jirgin na Kotoka.
Haka kuma hukumar ta zo ta kama hodar ibilis a filin jirgin na Kotoka da ta kai ta dala 300,000