Sojojin Isra'ila sun 'sace jarirai Falasdinawa sun fitar da su daga gaban iyayensu a Gaza . / Hoto: AA

0451 GMT — Dan majalisar Dattawa ya bukaci Amurka ta daina daukar nauyin yakin da Isra'ila ke yi a Gaza

Dan majalisar Dattawan Amurka Bernie Sanders ya nemi majalisar ta ki amincewa da tallafin $10.1bn na kayan yaki da kasar take so ta bai wa Isra'ila dominci gaba da "mummunan yaki" kan Falasdinawa.

"Bari na bayyana karara cewa: ba za a sake bayar da kudi domin haramtaccen yakin da Netanyahu yake yi kan al'ummar Falasduni ba," in ji Sanders a sakon da ya wallafa a shafin X.

Ya kamata Amurkawa su fahimci cewa Isra'ila na amfani da bama-bamai da sauran makaman Amurka ne wajen yin luguden wuta kan Falasdinawa, in ji shi, inda ya kara da cewa: "Hakan ya haifar da babban bala'i."

0200 GMT — An ji karar fashewar wasu abubuwa kusa da jirgin ruwa a gabar tekun Yemen a yayin da Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a Gaza

Hukumar kula da tsaron jiragen ruwa ta Birtaniya UKMTO ta ce an samu wata gagarumar fashewa kusa da jirgin ruwan daukar kaya a Zirin Bab al Mandeb, wanda ya raba Yankin Larabawa da Kusurwar Afirka.

Hukumar ta ce ta samu rahotanni na fashewar abubuwa har sau uku daga jirgin ruwan, wanda yake kan hanyarsa da ke tsakanin Eritrea da Yemen.

"Ba a samu rahoton lalacewar jirgin ruwan ba kuma a halin da ake ciki matukansa na cikin koshin lafiya," in ji hukumar kula da tsaron jiragen ruwa ta Birtaniya, wadda ke karkashin Rundunar Sojojin Ruwa ta Birtaniya, a wani takaitaccen sako da ta fitar.

Ta kara da cewa "hukumomi suna gudanar da bincike" kan lamarin.

A makonnin baya bayan nan, 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun kaddamar da jerin hare-hare da jirage marasa matuka da rokoki kan jiragen ruwan kasuwanci da ke wucewa ta Bahar Maliya da Zirin Bab al Mandeb wanda ya hada Bahar Maliya da Gabar Tekun Aden.

Sun ce suna daukar matakan ne domin nuna goyon baya ga Falasdinawa wadanda Isra'ila ke kai wa hare-hare babu kakkautawa a Gaza.

'Yan tawayen na Houthi sun yi gargadi cewa za su kai hari kan jiragen ruwan da ke da alaka da Isra'ila wadanda ke wucewa ta Bahar Maliya.

Wani Bafalasdine yana kuka a yayin da ya dauki gawar wani jariri daga Asibitin Al Aqsa bayan Isra'ila ta kai hari a sansanin 'yan gudun hijira da ke Nuseirat a Deir al Balah, a yankin Gaza ranar 2 ga watan Janairu, 2024. / Hoto: AA

0158 GMT — Faransa ba za ta goyi bayan kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa a Gaza ba

Faransa ba za ta goyi bayan kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza ba, a cewar Nicolas de Riviere, wakilin kasar na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.

"Faransa tana adawa da korar mutane daga matsugunansu da karfin tsiya. Wannan a bayyane yake...Ba za mu amince da korar mutane daga matsugunansu da karfin tuwo ba," in ji de Riviere a hira da manema labarai.

"A fili yake karara cewa Zirin Gaza wurin zaman Falasdinawa ne. Burinmu shi ne Falasdinawa su samu damar ci gaba da kasancewa cikin lumana da tsaro. Wannan shi ne babban burinmu."

0030 GMT — Sojojin Isra'ila sun 'sace jarirai Falasdinawa, sun fitar da su daga Gaza'

Sojoji Isra'ila sun sace wasu jarirai Falasdinawa sannan suka fitar da su daga Gaza, a cewar wata kungiyar da ke kare hakkin dan'adam, inda ta yi kira ga Isra'ila ta mayar da yaran wurin iyayensu.

Kungiyar Euro-Med Human Rights Monitor mai hedkwata a Geneva a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ta "dauki bayanin da aka watsa a Gidan Rediyon Sojojin Isra'ila ranar 1 ga watan Janairu na 2024 game da sace wata jaririya Falasdinawa daga gidansu a Gaza da wani sojan Isra'ila mai suna Harel Itach, da ke rundunar Givati tare da kashe iyayenta da matukar muhimmanci."

"Bayan samun labarin mutuwar wani sojan Isra'ila ranar 22 ga watan Disamba na 2023 sakamakon raunukan da ya samu a yakin Gaza, abokin Itach ya bayyana batun satar jaririyar inda ya ce ba a san inda take ba," in ji sanarwar.

Kungiyar ta nuna "matukar damuwa" game da hakan, tana mai cewa jaririyar ba ita kadai sojojin Isra'ila suka sace ba.

"Shaidu da dama da mutane suka nuna wa kungiyar kare hakkin dan'adam sun bayyana yadda sojojin Isra'la suke kama kananan yara Falasdinawa su tsare su, sannan su fitar da su daga yankinsu zuwa wani wuri da ba a sai ba," in ji kungiyar.

Jarirai da kananan yara suna samun mafaka a wata makaranta a Rafah
TRT Afrika da abokan hulda