Ana yawan samun matsalolin rushewar gine-gine a Nijeriya inda ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci. / Hoto: Others

Ɗalibai da dama na Jami’ar Benin sun maƙale a cikin wani gini mai hawa uku da ya rushe a Jihar Edo da ke Nijeriya.

Ginin wanda ke a Ekosodin, ya rushe ne da safiyar Asabar.

Rahotanni sun ce ginin ya rushe bayan an yi wani ruwa mai ƙarfi da safiyar ta Asabar.

Ekosodin na da iyaka da Jami’ar Benin, kuma yankin na da ɗalibai da dama da ke zaune.

Rahotanni sun ce duk da cewa har yanzu akwai wasu ɗalibai da ke maƙale, amma akwai waɗanda aka samu nasarar cetowa.

Ɗaya daga cikin ɗaliban da ke wurin da lamarin ya faru ya bayyana cewa wasu masu aikin ceto na jami’ar ta Benin sun ceto wasu da suka maƙale inda nan take aka kai su asibiti, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ana yawan samun matsalolin rushewar gine-gine a Nijeriya inda ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci.

Ko a kwanakin baya sai da aƙalla ɗalibai 22 suka mutu bayan ginin wata makaranta da ke tsakiyar birnin Jos ya rufta a kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa.

Aƙalla mutum 45 ne suka mutu a shekarar 2021 bayan da wani dogon bene da ake ginawa ya ruguje a gundumar Ikoyi da ke babban birnin tattalin arzikin Nijeriyar, Legas. S

annan mutum 10 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani gini mai hawa uku a unguwar Ebute-Metta da ke Legas shekara guda bayan haka.

TRT Afrika