‘Yan matan makarantar GSS Awon ta karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutane, in ji gwamnatin jihar.
Sanarwar da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar ranar Talata, ta ce 'yan matan, wadanda aka sace ranar 4 ga watan Afrilu, sun tsere ne daga cikin dajin da ke tsakanin jihohin Kaduna da Neja.
Sanarwar ta ce ‘yan matan sun yi tafiyar kwanaki kafin su samu mafaka a wani wuri da ba a ambata ba.
Bayan haka ne mutane suka ankarar da gwamnatin jihar wadda ta yi shirin kwashe yaran cikin gaggawa da hadin gwiwar sojoji.
"Masu garkuwa da mutanen sun yi ta neman ‘yan matan a cikin daji ba su same su ba don an riga an kwashe su," a cewar sanarwar.
A halin yanzu suna wani wuri na soji inda ake ba su kulawar da ta dace, a cewar sanarwar.
Gwamnan jihar, Nasiru El-Rufai ya sharwaci ‘yan matan su kara dagewa kan neman ilimi don samun makoma mai kyau, bayan ya yaba da karfin halin da suka nuna wajen tserewa daga masu garkuwa da mutanen.