Dakarun Kasa da Kasa na Hadin Gwiwa na yakar 'yan ta'addda a kan iyakokin Nijeriya, Nijar, Kamaru da Chadi. Hoto: AA

Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa ta Kasashen Yankin Tafkin Chadi (MNJTF) ta ce dakarunta sun kawar da 'yan ta'adda shida yayin da suka kai wa sojoji harin kwantan bauna a jihar Borno da ke arewacin Nijeriya.

Sanarwar da kakakin Rundunar Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar a birnin Ndjamena a ranar Alhamis, ta ce dakarun rundunar sun samu gagarumar nasarar kawar da 'yan ta'adda shida a yayin mayar musu da martani ga harin kwanton baunar da suka kai a yankin Binduldul na Jihar Borno, a kokarin da suke yi na kakkabe 'yan ta'adda daga yankunan.

Sanarwar ta ce "A yayin kai farmakin, dakarun sun gano mamakai da dama da suka hada da bindigogi biyu samfurin PKT da bindigogi biyar samfurin AK 47 da jigidar harsasai uku na AK 47 da kuma harsashai 239.

"An yi gagarumar nasara a kan 'yan ta'addar tare da lalata ayyukansu a yankin."

Kazalika sanarwar ta kara da cewa sojoji biyu sun samu raunuka a yayin kai farmakin, amma suna cikin yanayi mai kyau inda suke ci gaba da samun kulawa.

"Muna tare da su a zuci da baki kuma muna musu addu'o'inmu na tare da iyalansu, muna musu fatan farfadowa cikin sauri," in ji sanarwar.

A wani lamari mai alaƙa da wannan, a ranar 17 ga Oktoban nan, Bulama Bukar mai shekara 23 ya miƙa wuya ga jami'an tsaro a Gubio, Jihar Borno.

Bukar ya yi ikirarin cewa shi Kwamandan Boko Haram ne, a sansanin Tafkin Chadi da ke kauyen Gilima na Karamar Hukumar Abadam.

An bayyana cewa ya miƙa wuyan ne sakamakon ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Borno ke yi.

Sanarwar ta ce "Bayan mika wuyan, Bulama ya kuma miƙa wa jami'an tsaro bindiga samfurin AK 47 da kwanson ma'ajiyar harsashai biyar da harsashai na musamman masu girman milimita 7.62 guda 44, da kuma wasu kayayyaki."

Kwamandan Rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya yaba jarumta da sadaukarwar dakarun Kasa da Kasa na Hadin Gwiwa bisa nasarar kaddamar da farmakin.

TRT Afrika