Sojojin Mali dai na ci gaba da fafatawa da ƴan bindiga a yankunan yammacin kasar da ke makwabtaka da Burkina Faso da Nijar. / Hoto: Reuters  

Dakarun sojin Mali sun kashe ɗaya daga manyan kwamandojin ƴan ta'adda a yankin Sahel, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta sanar a ranar Talata.

An kashe Abu Huzeifa, wanda ake kira da Higgo a safiyar Lahadin da ta wuce a wani samame da aka kai yankin Menaka da ke arewacin ƙasar, kusa da iyaka da Nijar, a cewar sanarwar rundunar sojin.

Ya yi aiki a matsayin kwamandan sojin ƙungiyar ƴan ta'adda ta Daesh/ISIS a yankin iyakokin ƙasashen Sahel, Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.

Rahottanin sun bayyana cewa Huzeifa na da hannu a wani mumunar hari da aka kai a shekarar 2017 kusa da ƙauyen Tongo Tongo a Jamhuriyar Nijar inda aka kashe dakarun sojin Amurka na musamman guda hudu da na Nijar hudu.

Tukuicin Amurka

A sakamakon hakan ne Amurka ta saka tukuicin da ya kai dala miliyan 5 ga duk wanda ya samo mata shi ko yake da labarin inda yake.

Rundunar ta ce Huzeifa dan kasar waje ne, wasu rahotanni sun bayyana yiwuwarsa na zama ɗan asalin Jamhuriyar Sahrawi ne.

Rahotani sun ce ƙungiyar Huzeifa ta yi fice da kai hare-hare a yankin Menaka na kasar Mali, inda ake yawan zarginta da kai hari kan ƴan kasar ta Mali.

Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne suke da mafi yawan mace-macen mutane sakamakon ayyunkan ta'addanci a yankin, a cewar kididdigar rahoton 'Global Terrorism Index 2024' da Cibiyar Tattalin Arziki da Zaman Lafiya ta Australia ta fitar.

Kasashen uku dai na fuskantar matsalar tabarbarewar tsaro, inda kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaeda da Daesh/ISIS ke kaura daga kasar Mali zuwa yankuna makwabta da ke yankin na Sahel.

AA