Majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta sake zaɓen Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye bayan jam'iyyarsa ta African National Congress (ANC) ta ƙulla ƙawance da wasu jam'iyyun hamayya.
Mr Ramaphosa ya samu nasarar ce bayan ANC ta ƙulla ƙawance da jam'iyyar Democratic Alliance (DA) da wasu ƙananan jam'iyyu sakamakon kasa samun kashi 50 da take buƙata na kujerun majalisar dokoki a zaɓen ranar 29 ga watan Mayu abin da ya hana ta damar naɗa shugaban ƙasa ita kaɗai.
Shugaban ƙasar ya kayar da Julius Malema, shugaban jam'iyyar Economic Freedom Fighters.
A jawabin da ya gabatar bayan yin nasara, Mr Ramaphosa ya jinjina wa sabon ƙawancen da suka ƙulla, sannan ya ce 'yan ƙasar suna fatan shugabanni su yi "aiki tare domin ci gaban kowane ɗan ƙasa".
Wannan ne karon farko da jam'iyyar ANC ta haɗa gwiwa da wasu jam'iyyu don zaɓen shugaban ƙasa a cikin shekaru 30 da ta kwashe a kan mulki. Jam'iyyar ta samu kashi 40 na kujerun 'yan majalisar dokoki, yayin da jam'iyyar DA ta zo ta biyu inda ta samu kashi 22.
Ƙawance tsakanin ANC da DA ya bai wa kowa mamaki domin kuwa jam'iyyun biyu sun kwashe tsawon lokaci suna adawa da juna.
Sai dai a yayin da yake jawabi ga 'yan majalisar dokokin ranar Juma'a da tsakar dare a Cape Town, shugaban jam'iyyar DA, John Steenhuisen, ya ce: “Yau rana ce mai cike da tarihi ga ƙasarmu, kuma ina gani za ta buɗe wani sabon babi.”
Yanzu mataki na gaba da Mr Ramaphosa zai ɗauka shi ne na kafa majalisar zatarwarsa, wadda za ta ƙunshi mambobin jam'iyyar DA.