Cybersecurity levy: Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da fara aiki da harajin tsaro na intanet

Cybersecurity levy: Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da fara aiki da harajin tsaro na intanet

Ministan Watsa Labarai na ƙasar Mohammed Idris ne ya bayyana haka a shafinsa na X ranar Talata.
Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin ne a wajen taron Majalisar Zartarwa, a cewar Ministan Watsa Labarai na ƙasar, Mohammed Idris.

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa ta dakatar da sabon harajin nan na tsaron intanet, wanda za a ringa cirewa idan aka tura kuɗi ta banki zuwa wani asusun, wanda a Turanci aka fi sani da Cybersecurity Levy.

Ministan Watsa Labarai na kasar Mohammed Idris ne ya bayyana haka a shafinsa na X ranar Talata.

“Matsayin Gwamnatin Tarayya, daga taron Majalisar Zartawar na Ƙasa a jiya da yau shi ne, an dakatar da harajin cybersecurity levy,” a cewar sanarwar da ministan ya wallafa.

Wannan dai ya kawo ƙarshen jita-jitar da aka ringa yaɗawa tun ƙarshen makon jiya cewa, gwamnatin ƙasar ta dakatar da harajin, bayan ƙungiyoyi da dama da ma ɗaiɗaikun ‘yan ƙasar sun soki matakin fara aiki da sabon harajin, a lokacin da 'yan ƙasar ke kuka da halin matsin rayuwa.

Batun fara aiki da harajin dai ya janyo ce-ce-ku-ce, har ma wasu ƙungiyoyi irin su SERAP suka yi barazanar shigar da gwamnatin ta Nijeriya ƙara a kotu idan ba ta janye harajin ba.

Gyaran doka

Ita ma Majalisar Wakilan Ƙasar ta yi kira ga Babban Bankin Ƙasar (CBN) ya dakatar da fara aiki da sabon harajin, saboda a cewar majalisar matakin zai ƙara jefa 'yan ƙasar cikin halin ƙuncin rayuwa da ake fama da shi.

A saƙon da ya wallafa a shafin nasa na sanarwar dakatar da harajin, Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris ya ce, “za a sake nazartar” harajin.

Ɗaya daga 'yan Majalisar Dattijan Ƙasar da tun da farko suka nuna rashin amincewa da sabon harajin Sanata Ali Ndume ya ce sun yaba wa Shugaba Tinubu bisa dakatar da fara aiki da sabon harajin.

"Wannan ya nuna cewa Shugaban yana sauraron jama'a," in ji Sanata Ndume a tattaunawarsa da TRT Afrika Hausa.

Sanatan ya ce yanzu za su mayar da wannan doka majalisar ƙasa, don sake yi mata duban tsanaki da kuma yi mata gyara.

TRT Afrika