Gwamnatin Chadi ta bai wa jakadan Jamus Gordon Kricke umarni ya fita daga kasar cikin kwana biyu.
Ma’aikatar Watsa Labaran kasar ce ta bayar da umarnin a wani sako da ta wallafa a shafint na Twitter ranar Juma’a.
"Wannan mataki da gwamnati ta dauka ya faru ne saboda halayen rashin dattako da rashin mutunta al’adar diflomasiyya," in ji sanarwar.
Sai dai wata majiya a ofishin jakadancin Jamus da ke kasar ta shaida wa kamfanin dillancin labaai na AFP cewa gwamnatin Chadi ba ta tuntube su game da batun ba, tana mai cewa sun ga sanarwar ce a shafukan soshiyal midiya.
Kricke ya taba zama jakadan Jamus a Jamhuriyar Nijar, Angola da Philippines.
Chadi ta saki ‘yan tawaye 380 da aka daure bisa zargin kashe Idriss Deby
Kazalika ya rike mukamin wakilin Jamus na musamman a yankin Sahel mai fama da rikici.
Wata majiyar gwamnati da ba ta so a ambaci sunanta ta shaida wa AFP cewa ana kallon Kricke a matsayin mutumin da ke "katsalandan sosai" a harkokin gwamnati da yin kalaman da ke raba kawunan jama’a.
Ta kara da cewa sau da dama ana gargadinsa amma bai ji ba.
Sukar gwamnati
A cewar kamfanin dillancin labarai na Chadi, Kricke yana cikin fitattun mutanen da suka goyi bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati ta watan Oktoban 2022 wacce ta yi sanadin mutuwar gwamman mutane sakamakon arangama tsakanin su da jami'an tsaro.
A watan Fabarairu, Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Chadi ta ce mutum 128 sun mutu a jerin zana-zangar, adadin da ya ninka wanda gwamnati ta sanar.
Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya hau mulkin kasar ne bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby Itno, a fagen daga a watan Afrilun 2021.
Deby ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu lokacin fafatawarsu da 'yan tawaye bayan ya shekara fiye da 30 ana mulki.
A watan jiya, shugaban kasar ya gafarta wa fiye da mutum 200 da ake zargi da hannu a kisan mahaifinsa watanni hudu bayan an same su da laifi, kuma a wannan makon aka sallame su.