A ranar Laraba gwamnatin ƙasar Chadi ta lashi takobin kakkaɓe ayyukan Boko Haram bayan wani ƙazamin hari da mayaƙan ƙungiyar suka kai wani barikin sojin ƙasar a ƙarshen mako.
Mayaƙan Boko Haram sun kashe kusan sojoji 40 tare da jikkata da dama a wani samame da suka kai ranar Lahadi a sansanin da ke yankin Tafkin Chadi, inda ake fama da hare-haren ƙungiyoyi daban-daban masu ɗauke da makamai.
A martanin da ta mayar, Chadi a ranar Litinin ta ƙaddamar da harin Operation Haskanite, "da nufin tabbatar da zaman lafiyar al'ummarmu" har ma da "farauta da kawar da ƙungiyar Boko Haram da matsalolinta da masu alaƙa da ita", kamar yadda Firaminista na wucin-gadi Abderahim Bireme Hamid ya shaida wa 'yan jarida a N'Djamena.
Ministan Harkokin Wajen Chadi Abderaman Koulamallah shi ma a ranar Laraba ya sake sabunta kiran da al'ummar ƙasar ke yi ga ƙasashen duniya da su ƙara zage damtse wajen tallafa wa yaƙi da ta'addanci a yankin.
A yankin mai yalwar ruwa da fadamu, tsibiran yankin Tafkin Chadi marasa adadi sun zama maɓoya ga ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, irinsu Boko Haram da ƙungiyar IS da ke Yammacin Afirka (ISWAP), waɗanda ke kai hare-hare a-kai-a-kai kan sojojin ƙasar da ma fararen-hula.
Ƙungiyar Boko Haram ta fara ƙaddamar da hare-hare a Nijeriya a shekara ta 2009, waɗanda suka yi sanadiyar mutuwar mutum fiye da 40,000 tare da raba miliyan biyu da muhallansu, kuma ƙungiyar ta yaɗu zuwa ƙasashe maƙwabta.
A watan Maris na shekarar 2020, sojojin ƙasar Chadi sun yi asara mafi girma ta kwana guda a yankin, lokacin da sojoji kusan 100 suka mutu a wani samame da suka kai a gabar Tafkin Bohoma.
Gwamnati, kamar yadda ta yi a wancan lokacin, ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki na ƙasa daga ranar Talata, tare da yin ƙasa-ƙasa da tutoci da kuma haramta bukukuwa.