An kashe mahaifin Deby a fagen daga bayan ya mulki kasar tsawon shekaru talatin  Hoto\AA

Gwamnatin Chadi ta saki daruruwan ‘yan tawayen kasari da aka daure bisa zarginsu da hannu wajen mutuwar tsohon shugaban kasar Idriss Deby Itno.

An sallame su ne bayan sun kwashe shekaru biyu a tsare.

Mambobin kungiyar ‘’Front for Change and Concord’’ FACT a Chadi su 380 shugaban rikon kwarya Mahamat Idriss Deby Itno ya yi wa afuwa a watan jiya.

A ranar Laraba, Ministan Shari'ar kasar, Mahamat Ahmat Alhabo ya jagoranci wani biki na sakin su.

An ba su takardun shaida na sakin 'yan tawayen daga gidan yarin Klessoum da ke kusa da babban birnin kasar N'Djamena, a cewar kamfanin dillancin labarai mai zaman kansa a Chadi

Wadanda aka sako suna daga cikin mutane 400 da aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai a ranar 21 ga watan Maris bisa zarginsu da hannu a mutuwar Idriss Deby Itno, mahaifi ga shugaba mai rikon kwarya na kasar.

An yi musu shari’a kuma aka same su da laifukan ta’addanci da yin zagon-kasa ga tsaron kasa da jefa rayuwar shugaban kasa cikin hadari da kuma daukar kananan yara aiki da dai sauransu.

An saki mutanen ne don "su yi nazari" kan laifukan da aka tsare su akai su kuma canja munanan halayensu," in ji Alhabo.

Sakin 'yan tawayen na daga cikin "alkawarin" da shugaban kasar ya yi a bara, a wajen wani taron samar da zaman lafiya na kasa don 'yantar da 'yan kungiyoyin ta’addanci a karkashin shirin afuwa don samar da tattaunawa a Chadi.

Shugaban kungiyar Mahamat Ali Mahadi, wanda ba a kama ba amma aka yanke wa hukuncin daurin rai- da-rai, ba ya cikin wadanda suka samu wannan rahama.

Kasar Chadi ta bai wa hukumomin duniya sammacin kama Mahadi.

A watan Janairun 2022, gwamnatin rikon kwarya a kasar ta saki wasu mambobin kungiyoyin ta'addanci 250 da aka yanke wa hukunci kan zargin kai wa gwamnati hari da makamai/

Tun a watan Afrilu 2021 aka kama 'yan tawayen kungiyar FACT yayin arangama da suka yi da sojoji a arewacin Chadi

An kashe mahaifin Deby, wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru talatin, a fagen daga.

Daga nan ne aka kafa majalisar soji karkashin ikon dansa Mahamat Deby domin rikon kwarya na tsawon watanni 18 a kasar.

A watan Oktoban da ya gabata ne ya kamata ya mika mulki, amma wa’adin bai cika ba, ya zama shugaban rikon kwarya.

Soji sun tsawaita wa’adin mika mulki da shekaru biyu, inda a watan Oktoban shekarar 2024 aka shirya gudanar da zabe.

Matakin ya haifar da zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma.

TRT Afrika da abokan hulda