Sauran kasashen Yammacin Afirka biyu na G5 Sahel a ranar Laraba sun tabbatar da cewa suna sharar fage domin ficewa daga rundunar yaki da ta’addanci bayan sauran kasashen uku sun fice.
G5 Sahel, wadda ta kunshi Mauritania da Chadi da Burkina Faso da Mali da Nijar, an kafa ta ne a 2014 inda a 2017 ta kafa runduna ta yaki da ta’addanci karkashin goyon bayan Faransa.
A ranar Asabar, Burkina Faso da Nijar suka bayyana cewa za su janye daga yarjejeniyar, inda dama ita Mali tun a 2022 ta sanar da cewa za ta fice.
A cikin wata sanarwa da kasashen biyu suka fitar sun ce, kasashen Chadi da Mauritaniya “sun yi la'akari da mutunta matakin da kasashen Burkina Faso da Nijar suka dauka” na ficewa daga kawancen, tare da bin sahun Mali.
Za su “aiwatar da duk wasu matakai da suka dace da kundin tsarin G5 Sahel, musamman sashe na 20,” a cewarsu.
Sashen ya bayyana cewa za a iya kwance kawancen da zarar uku daga cikin mambobin kungiyar sun amince.
A lokacin da suke sanar da janyewarsu a ranar Asabar, sojojin da ke mulkin Burkina Faso da Nijar ba su fito karara sun yi kira da a rusa ta ba.
Sai dai da alama makomar kungiyar ta kasance a rufe tun kafin gwamnatin mulkin sojan Mali ta sanar da cewa za ta yi murabus a shekarar 2022.
Sai dai da alama tuni aka kammala tsyar da makomar kungiyar tun kafin sojojin na Mali su sanar da janyewarsu a 2022