Burkina Faso ta zargi maƙwabciyarta Ivory Coast kan ba da mafaka ga "masu tayar da zaune tsaye"

Burkina Faso ta zargi maƙwabciyarta Ivory Coast kan ba da mafaka ga "masu tayar da zaune tsaye"

Dangantaka tsakanin ƙasashen yammacin Afirka biyu maƙota ta yi tsami, duk da tattaunawa tsakanin hafsoshin tsaro na ƙasashen.
Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore ya ce alhakin Ivory Coast ne ta warware takun-saƙar. / Hoto: Reuters

Shugaban mulkin soji na Burkina Faso, Ibrahim Traore ya zargi ƙasar Ivory Coast ranar Juma'a, kan yin maraba da "duka masu tayar da zaune tsaye" na ƙasarsa, inda ya ƙara da cewa akwai "matsala tattare da mahukunta" a Abidjan.

Dangantaka tsakanin ƙasashen yammacin Afirka biyu maƙota ta yi tsami a 'yan kwanakin nan, kuma ranar 19 ga Afrilu hafsoshin tsaro na ƙasashen biyu sun tattaunawa kan iyaka a ƙoƙarin sake "sabunta kyakkyawar" alaƙa.

Da yake magana game da Ivory Coast a wata hira da gidan talabijin na ƙasar, RTB, Traore ya ce: "Duk masu tayar da zaune tsaye suna can, kuma ba sa ɓoye kansu".

Ya ƙara da cewa, "Za a zo lokacin da sai mun dakatar da munafurcin mun faɗi gaskiya - akwai matsala da mahukuntan wannan ƙasa".

'Babu mu'amala ta musamman'

Gwamnatin Traore ta karɓi iko a juyin mulkin 2022 kuma tun daga sannan ta nesanta kanta daga ƙasar da ta mata mulkin mallaka, Faransa kuma ta zaɓi ƙarfafa dangantakar soji da gwamnatocin soji a yankin, da kuma Rasha.

Da yake jawabi kan sugaban Ivory Coast Alassane Ouattara, Traore ya ce ba shi da wata 'mu'amala ta musamman' da shi.

"Da fari mun yi magana kaɗan ta waya, ya turo min jakadu muka tattauna, mun yi fatan abubuwa za su tafi yadda ya kamata," sai ya ƙara da cewa, "wannan ya rushe" yanzu.

Game da taron da aka yi tsakanin hafsoshin tsaro na ƙasashen biyu, Traore ya ce "ya rage garesu", kuma ya ce "taron ya tafi daidai".

Ya kuma ce, "Mun yi ganawar ƙeƙe-da-ƙeƙe. Muna kallonsu yanzu".

Tsamin dangantaka

Dangantaka tsakanin Ivory Coast da Burkina Faso, wadda ke fama da ƙungiyoyin ta'adda, ta samu tasgaron rashin jituwa.

A ƙarshen Maris, an kama wani sojan Burkina Faso da jami'in farar hula a arewacin Ivory Coast.

Sannan a Satumbar bara, an kama 'yan sandan Ivory Coast guda biyu a yankin Burkina a wani haramtaccen wajen haƙar zinare.

Tattaunawa na ci gaba game da sakin 'yan kasashen biyu da ke hannun kowannensu.

TRT Afrika