Burkina Faso ta saki 'yan ƙasar Faransa huɗu bayan shiga tsakani da ƙasar Maroko ta jagoranta, kamar yadda Marokon ta tabbatar a ranar Alhamis.
Shugaban DGSE wadda ita ce hukumar leƙen asiri ta Faransa a baya ya sanar da cewa mutanen uku 'yan leƙen asiri ne.
Wani mai magana da yawun sojin Faransa, wanda ke kula da DGSE, da kuma ita kan ta hukumar ta DGSE ba su mayar da martani kan lamarin ba.
Ana tsare da 'yan leƙen asirin a Ouagadougou tun daga Disambar 2023.
Fadar Shugaban Faransa a wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa Shugaba Emmanuel Macron a ranar Laraba ya gode wa Sarkin Marokon Mohammed kan shiga tsakaninsa "wanda ya ba da damar 'yantar da 'yan kasarmu hudu da aka yi a Burkina Faso tsawon shekara guda".
'Aikin jin ƙai'
Ma'aikatar Harkokin Wajen Maroko ta jinjina wa Sarko Mohammed da kuma Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore tare da cewa "wannan aikin jin ƙai" ya tabbata ne sakamakon dangantaka mai kyau a tsakanin ƙasashen.
Bayan shafe shekara uku ana zaman ɗar-ɗar tsakanin Paris da Rabat wanda matsalolin baƙin haure suka haddada da kuma yankunan da ake rikici a kansu a Yammacin Sahara, Faransa ta sasanta da Maroko a Oktoba wadda tana daga cikin ƙasashen da ta mulka.
Maroko na da kyakkyawar alaka da Burkina Faso da sauran ƙasashen Sahel da sojoji ke mulkin kasar, inda ta yi musu alkawarin samun damar yin kasuwanci a duniya ta Tekun Atlantika.
Sai dai alakar Faransa da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka ciki har da Burkina Faso na ci gaba da yin tsami.
Ouagadougou ta kori sojojin Faransa da jami'an diflomasiyya, sannan ta umarci wakilin tsaro na Faransa da jakadan kasar da su fice, sannan ta dakatar da wasu kafafen yada labaran Faransa.