Ƙasashen uku suna so Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauki  ''matakan da suka dace'' a kan Ukraine, suna masu cewa tana ''ƙarfafa gwiwar ƙungiyoyin ta'addanci a Afirka.”Hoto/ @PresidenceMali/X

Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar sun kai ƙarar Ukraine a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Talata inda suka zargi gwamnatin ƙasar da fitowa “fili tana goyon bayan ƙungiyoyin 'yan ta'adda na duniya" musamman a yankin Sahel.

Ƙasashen uku sun ɗauki matakin ne bayan wasu kalamai da jami'an diflomasiyyar Ukraine suka yi a kwanakin baya da ke nuna rawar da ƙasarsu ta taka a hare-haren da Abzinawa 'yan tawaye suka kai wa sojojin Mali a watan jiya a yankin Tinzawaten na kan iyaka da Algeria inda suka kashe sojoji da dama.

A wata wasiƙa da ministocin ƙasashen uku suka aike wa Kwamitin Tsaro na MDD, sun bayyana matuƙar kaɗuwarsu bisa kalaman da mai magana da yawun rundunar leƙen asirin Ukraine Andriy Yusov, ya yi cewa, “na amincewa da rawar da Ukraine ta taka a hare-haren dabbanci kuma na matsorata da masu aikata lafuka suka kai wa" dakarun Mali daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Yuli.

Wasiƙar ta ƙara da cewa jakadancin Ukraine a Senegal Yurii Pyvovarov shi ma ya tabbatar da rawar da ƙasarsa ta taka wurin kai wa sojojin Mali hari.

Yusov ya ce 'yan tawayen sun samun "dukkan bayanan da suke buƙata" domin kai hari kan sojojin Mali da abokansu sojojin haya na Wagner na ƙasar Rasha. Sojojin na Wagner na cikin waɗanda 'yan tawayen suka kashe, a cewar hukumomi.

Ƙasashen uku sun yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauki ''matakan da suka dace'' a kan Ukraine, saboda matakin da ta ɗauka na ''ƙarfafa gwiwar ƙungiyoyin ta'addanci a Afirka.”

''Waɗannan ayyuka sun keta 'yancinmu na kasancewa ƙasashe masu cin gashin kawunansu, kuma ya nuna ƙarara yadda aka yi kutse tare da goyon bayan ƙungiyoyin ta'addanci na duniya, lamarin da ya saɓa wa Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran dokokin ƙasashen duniya," in ji wasiƙar.

AA