Kawancen wani bangare ne na ci gaba da tattaunawar da aka soma tsakanin Shugaba Putin da Shugaba Traore a taron Rasha da Afirka da aka yi a St. Petersburg a watan Yuli./Hoto:Reuters

Wata tawagar Rasha ta tattauna da shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore ranar Alhamis kan batutuwa da dama ciki har da hadin-gwiwa game da ayyukan soji.

Fadar shugaban kasar Burkina Faso ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce ziyarar da mataimakin ministan tsaron Rasha Yunus-Bek Yevkurov ya jagoranta zuwa Ouagadougou wani bangare ne na ci gaba da tattaunawar da aka yi tsakanin Traore da shugaban Rasha Vladimir Putin a taron Rasha da Afirka da aka yi a St. Petersburg a watan Yuli.

Kawancen Burkina Faso da Moscow ya ja hankalin duniya tun bayan da kasar ta kori dakarun Faransa a watan Fabrairu, lamarin da ya sa aka rika jita-jita cewa za ta kyautata dangantaka da Rasha kan harkokin tsaro kamar makwabciyarta Mali, inda sojojin haya na Wagner suke gudanar da ayyukansu.

Taron ya tattauna kan "hanyoyi da za a hada kai wadanda suka shafi aikin soji, ciki har da horar da dakarun Burkina Faso a kowane mataki, da suka hada da matuka jirgin sama a Rasha," in ji sanarwar.

Sanarwar ba ta yi bayani kan ko Rasha za ta tura sojojinta Burkina Faso don bai wa dakarun kasar horo ba.

Wannan ziyara wata karin alama ce da ke nuna irin tasirin da Moscow take ci gaba da yi a Afirka bayan mutuwar shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin, kungiyar da ta kulla kawance a Afirka da wasu bangarorin duniya.

Reuters