Buhari

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya nemi gafarar mutanen da ya bata wa rai a sakonsa na sallah ta karshe a matsayin Shugaban Nijeriya kafin ya mika mulki ga gwamnati mai jiran gado.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta Ambato Shugaba Buhari yana cewa: “Allah ya ba ni wata dama ta musamman ta yi wa kasar hidima. Dukkanmu ‘yan Adam ne, idan na bata wa wani yayin da nake yi wa kasa hidima na nemi a gafarce ni.”

Sanarwar da babban mai taimaka wa Shugaban kasar kan watsa labarai, Garba Shehu ya fitar ta ce Buhari ya yi wannan maganar ne a lokacin da mutanen Abuja babban birnin kasar suka kai wa Shugaba Buhari gaisuwar sallah karkashin jagorancin ministan Abuja, Muhammed Musa Bello.

Shugaban ya shaida wa wadanda suka kai masa gaisuwa sallah cewar shi zai koma Daura don ya huta da zaran ya ajiye mulki/Hoto:Nigerian Government

Shugaban ya ce shi ya yi maraba da koke-koke da suka da aka yi masa ba tare da fushi ba don shi ya san abubuwa dake tare da shugabancin da ya roki Allah ya ba shi.

Shugaba Buhari ya gode wa ‘yan Nijeriyar da suka zabe shi a shekarar 2015 da shekarar 2019, ba tare da am ba su wani kudi na jan hankalinsu ba, da kuma wadanda suka yi ta tururuwa zuwa wuraren gangamin yakin neman zabe don kawai su ganshi.

Shugaba Buhari, wanda wa’adin mulkinsa ya rage kimanin wata daya ya yi bayani kan irin abubuwan da ya gani a lokacin ya yi wa kasar hidima tun yana soja har ya zama farar hula, yana mai cewa yanzu komawa Daura zai yi don ya huta.

Shugaba Buhari ya ce a da rashin tsaro ya mamaye birnin tarayyar Nijeriya da ma kasar gabadaya/Hoto:Nigerian Government

“Na kosa in koma gida a Daura. Idan suna son su dame ni da surutu a Daura, zan koma Jamhuriyar Nijar. Da gangan na yi tanadin kasance da nisa yadda ya sauwaka. N samu abin da nake so kuma zan koma garinmu cikin a hankali,” a cewar shugaban.

Buhari ya yaba wa tsarin mulkin dimokradiyya wanda y ace ya bai wa irinshi da yake daga kan iyakar Nijeriya ya mulki kasar na tsawon shekara takwas.

“Garinmu, Daura, bai wuce kimanin kilomita takwas zuwa Jamhuriyar Nijar ba,” kamar yadda sanarwar ta ambato shugaban yana cewa.

Shugaba Buhari ya ce amfani da kabilanci da addini a siyasa ba shi da amfanim, inji sanarwar da ta fito daga fadar shugabn kasar/Hoto:Nigerian Government

“Abu mai kyau ne a yi tunani kan ababen dake faruwa a nan, babban birnin tarayya, musamman kan harkar tsaro. Maganar tsaro ba ta takaice a arewa maso gabas kawai ba ta kai birnin tarayya da duk fadin kasar nan,” in ji shi.

“Wadanda suke so su samu rayuwarmu cikin wani mawuyacin hali sun kai birnin tarayya, kuma yanzu an kaskantar da su,” a cewarsa.

Ranar 29 ga watan Mayu ne Shugaba Buhari zai mika mulki ga Bola Ahmed Tinubu na ja’iyyarsa ta APC wanda ‘yan Nijeriya suka zaba a zaben da aka gudanar cikin watan Fabrairun shekarar 2023.

Shugaban kasar mai barin gado ya ce shi ya yi maraba da suka da koke-koen da aka yi don shi ya san mulkin da ya roka daga Allah yana tare da su/Hoto: Nigerian Government
TRT Afrika da abokan hulda