Shugaban kamfanin Bua Abdul Samad Rabiu ya sha alwashin karya farashin siminti tun lokacin da ya gana da shugaban Nijeriya Bola Tinubu a kwanakin baya./Hoto: Bua  Cement Plc

Kamfanin BUA Cement Plc da ke Nijeriya ya sanar da rage farashin buhun siminti daga sama da naira dubu biyar zuwa Naira 3,500.

Kamfanin ya bayyana haka ne ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta.

Sanarwar ta ce: "A wani bangare na shirinmu na rage farashi kuma sakamakon sauyin da muka samu na inganta kasuwancinmu, rukunin kamfanonin BUA Cement Plc yana sanar da kwastomominmu da dukkan jama'a cewa daga ranar 2 ga watan Oktoba, 2023 mun yanke shawarar karya farashin (siminti).

Don haka, yanzu kamfanin siminti na BUA zai rika sayar da buhun siminti daya a kan Naira 3,500 ( farashin kamfani) domin 'yan Nijeriya su soma cin moriyar karya farashin kafin mu kammala gina kamfaninmu".

Labari mai alaka: Daidaita farashin dala mataki ne mai kyau – BUA

BUA ya kara da cewa da zarar ya kammala sabon kamfanin simintinsa, wanda zai rika samar da metirik ton miliyan 17 a duk shekara, zai sake karya farashin simintin zuwa kasa da yadda yake a yanzu.

A kwanakin baya ne shugaban kamfanin BUA Abdul Samad Rabiu ya sha alwashin karya farashin siminti lokacin da ya gana da shugaban Nijeriya Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

TRT Afrika