Majalisar Dattijan Nijeriya ta gayyaci Nuhu Ribadu da shugabannin hukumomin tsaro kan zargin cewa USAID na tallafa wa ayyukan Boko Haram.

Majalisar Dattijan Nijeriya ta nemi Babban Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribado da Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Nijeriya NIA da Sashen Tattara Bayanan Sirri na hedkwatar tsaron Nijeriya (DIA) kan zarge-zargen da aka bijiro da su cewa Hukumar Amurka da ke Taimakon Kasashen Waje (USAID) tana ɗaukar nauyin ta'addanci.

Kiran a gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin ba da tallafin ta'addanci da ake yi wa hukumar ta USAID ya biyo bayan kudirin da Sanata Ali Ndume ya gabatar a kan bukatar gaggawar yin binciken lamarin.

A yayin wani zaman majalisar, ‘yan majalisar sun nuna damuwarsu kan wani bidiyo na wani dan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, wanda ya yi zargin cewa hukumar USAID na da hannu wajen tallafa wa kungiyoyin ta’addanci a duniya ciki har da Boko Haram.

Ndume ya bayyana cewa, wannan ikirari na zuwa ne jim kadan bayan babban hafsan hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa, ya nuna fargabar cewa kungiyoyin ta’addanci a kasar na samun tallafi da horo daga kungiyoyin kasa da kasa.

A watan Janairu, shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da duk wani tallafin da ake bai wa ƙasashen ƙetare, yana mai bayanin cewa dakatarwar ita ce ta tantance ko amfani da wadannan kudade ya yi daidai da muradun Amurka.

TRT Afrika