Betta Edu, wadda tsohuwar shugabar mata ce ta jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya, ta musanta aikata ba daidai ba./Hoto:  Ma'aikatar Jinkai ta Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a Ma'aikatar Jinkai wadda ke karkashin Betta Edu kan zargin badakalar miliyoyin kudade.

Shugaban kasar ya bayar da umarnin ne ranar Lahadi da maraice, kamar yadda wata sanarwa da Ministan Watsa Labarai na kasar Mohammed Idris, ta sanar.

An yi ta ce-ce-ku-ce a kasar bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta Nijeriya ta tura naira miliyan 585 ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi na shirin bayar da kudi ga marasa galihu.

Sai dai Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta ce ofishinta ba ya biyan kudi a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa.

Hakan ya karfafa zargin da ake yi wa Betta Edu na yunkurin karkatar da kudaden gwamnati zuwa asusun daidaikun jama’a.

Amma sanarwar da Ministan Watsa Labarai ya fitar ta ce gwamnati na sane da abin da ke faruwa a Ma'aikatar Jinkai kuma za ta yin cikakken bincike don gano hakikanin gaskiya.

“A kan haka ne, shugaban kasa ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya da sahihancin wadannan rahotanni,” in ji Mohammed Idris .

Ya kara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu “tana gudanar da lamuranta a fayyace” don haka za ta dauki matakin da ya kamata idan ta gama bincikenta.

TRT Afrika