Benin ta kaddamar da sabbin lambobin yabo don karrama sojojin da suka yi bajinta. /Hoto: TRTAfrika

Gwamnatin kasar Benin ta bullo da wasu sabbin lambobin yabon soji biyu don jinjina wa dakarunta a daidai lokacin da suke kara fuskantar barazana daga makaya masu ikirarin jihadi a kan iyakar arewacin kasar.

Wannan yunkuri ya nuna irin gwagwarmayar da kasar ke yi wajen shawo kan hare-haren da ke bazuwa daga yankin arewacin Sahel zuwa kasar Benin, inda mayakan da ke da alaka da kungiyar IS da kuma Al-Qaeda suke zafafa kai hare-hare.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar Laraba ta ce za a bayar da lambobin yabon biyu - 'National Defence Medal' da 'Combatant's Cross' ga jami'an tsaro da mutanen da suka yi wa kasa hidima ta hanyar yaki domin zama abin kwatance da kuma karfafa gwiwar 'yan baya wajen sadaukar da kai ga ci-gaban kasa,

Lambar yabo ta wadanda suka yi wa kasa hidima ta hanyar yaki 'Combatant's Cross' za a ba da ita ga sojojin da aka kashe ko kuma wadanda suka jikkata a fagen yaki.

''An tsara lambobin yabo ne domin karfafa gwiwar jami'an tsaron kasar Benin wadanda ba su fuskanci yaki ba tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekarar 1960," a cewar masanin kimiyyar siyasa kuma kwararre kan harkokin tsaro a Benin, Odilon Koukoubou.

"Ba a cika jinjina wa sojojin ba a fagen kare kasa daga makiyanmu na waje," in ji shi.

Koukoubou ya kara da cewa "A halin da ake ciki yanzu al'amura na canjawa bayan barazanar sake bullowar hare-haren ta'addanci a kan iyakokin arewacin kasar."

Gwamnatin Benin ta dauki matakan tallafa wa dakarunta wadanda suka mutu ko kuma suka jikkata a fagen daga.

Basafai hukumomi ke bayani kan hare-haren masu ikirarin jihadi a arewacin Benin da ke kan iyakar kasar da Burkina Faso da Nijar ba.

A watan Afrilu shekarar nan, sojojin Benin sun bayyana cewa tun daga shekarar 2021 sun fuskanci zafafan hare-hare kusan 20 daga kan iyakokin kasar.

Janyewar sojojin Faransa daga yankin Sahel ya kara fargabar da ake yi game da yanayin tsaro a kan iyakokin Benin da Gabar Tekun Guinea da ke makwabtaka da kasar Ghana da Togo da kuma Ivory Coast.

A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Benin ta dauki matakan tallafa wa dakarunta.

A makon da ya gabata ta zartar da wata doka da za ta samar wa iyalan sojojin da aka kashe ko suka bata a yayin yi wa kasa hidima tallafin da za su iya dogaro a kai.

Sannan a farkon wannan shekara ne ta kaddamar da shirin daukar wasu karin sojoji 5,000 don taimakawa wajen karfafa tsaron iyakokin kasar.

TRT Afrika da abokan hulda