Shugaban rundunar da ke tsaron shugaban Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani, a ayyana kansa a matsayi sabon shugaban kasar.

A ranar Juma'a ne Janar Abdourahmane Tchiani ya bayyana a gidan talabijin na kasar Nijar sannan ya ayyana kansa a matsayin shugaban Majalisar Ceton Kasa, wata rundunar soji da ta sanar da hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar Alhamis.

Janar din, wanda ake kuma kiransa da Omar, ya ce kasar na bukatar ta sauya turbar da take kai don guje wa "durkushewar" da take fuskanta, don haka ya yanke shawarar shiga lamarin.

Wane ne Tchiani?

Janar Tchiani shi ne kwamandan rundunar sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa.

Rahotannin kafafen watsa labarai da dama sun bayyana shi a matsayin shugaban juyin mulkin, bayan da mambobin tawagarsa a ranar Laraba suka tsare Shugaba Bazoum a cikin fadar shugaban kasa.

Janar din mai shekara 62 shi ne shugaban sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa tun 2011, kuma a shekarar 2018 ne tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya yi masa karin girma.

A bisa tsari, ana kafa rundunar masu gadin fadar shugaban kasa ne don su dinga bai wa shugaban kasa kariya daga yi masa juyin mulki.

Sai dai ba wannan ne karo na farko da ake alakanta Tchiani da kokarin aiwatar da juyin mulki ba.

An taba zarginsa da kasancewa cikin wadanda suka yi kokarin kitsa juyin mulki ga Shugaba Issoufou a shekarar 2015, amma daga baya aka wanke shi daga zargin.

Tun ranar Laraba ba a sake ganin Shugaba Bazoum a bainar jama'a ba, amma dai ya yi magana ta waya da Sakataren Harkokin Wajen Amurka da kuma Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.

Ya ce "ana iya samun sa kuma yana cikin koshin lafiya," kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Faransa ya fada.

Me shugaban juyin mulkin yake so?

Da yake magana a gidan talabijin na kasar a ranar Juma'a, Janar Tchiani ya ce sojoji sun kwace mulki ne saboda abin da ya kira tabarbarewar al'amura a kasar.

Ya ce kasar na bukatar sauya turbar da take kai don gujewa "rushewa a hankali a hankali" don haka ne shi da sauran sojoji suka yanke shawarar daukar mataki.

"Na yi magana da abokan huldarmu na tattalin arziki da fasaha wadanda kawayen Nijar ne da su fahimci irin halin da kasarmu ke ciki don su taimaka mana da dukkan taimakon da muke bukata wajen magance matsalolin," ya ce.

Kungiyar Tarayyar Turai ta mayar da martani kan rokon ta hanyar yin barazanar yanke agajin da take bai wa kasar.

"Dole ne Nijar ta fuskanci ba daidai ba daga EU kan duk wata take dokar tsarin mulki, ciki har da dakatar da dukkan tallafin kudade da take samu," a cewar wata sanarwa da ta fito daga kungiyar ta EU mai mambobin kasashe 27.

TRT Afrika