Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya nesanta kansa da wani labari da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa ya ce ya fi ƴan Nijeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya ce “wasu ne suka ɗauki nauyin yaɗa labarin domin ɓata mini suna, a daidai lokacin da ƴan Nijeriya ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda wahalhalun da ake fama da su,” kamar yadda sanarwar da kamfaninsa ya fitar ta bayyana.
Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya nemi ƴan ƙasar su yi watsi da labarin, inda ya yi fatan kawo ƙarshen matsalar da ake ciki a Nijeriya.
"Duk abin da ya shafi ƴan Nijeriya ya shafe mu", in ji sanarwar.
Matsalar hauhawar farashi da tsadar rayuwa da matsi na ci gaba da ta’azzara a Nijeriya, inda ko a makon da ya wuce wasu al’umma suka yi zanga-zanga a jihar Neja da nufin jawo hankalin gwamnati kan lamarin.
Sai dai gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suna ta lallashin ƴan ƙasar tare da alƙawarin cewa abubuwa za su yi sauƙi nan ba da jimawa ba.
A sanarwar kamfanin nasa, Dangote ya ƙara da cewa, ''an kawo maganar faɗuwar darajar Naira da sayen kaya da Dala ne domin cim ma wasu buƙatu na ƙashin kai buƙatun da ba a samu damar biya ba a baya."
"Mu ma muna sayen muhimman kayan abinci a kasuwa kamar yadda kowa ke saya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al'umma," in ji Dangote.
Shugaban kamfanin ya kuma bayyana mamaki kan yadda ake neman haddasa saɓani tsakanin Kamfanin Dangote da gwamnatin tarayya, inda ya ce shi ɗan kasuwa ne ba ɗan siyasa ba, don haka babu inda ya yi maganar ƙalubalantar gwamnati.
"Kamfaninmu ya kasance mai bin dokokin ƙasa a ko da yaushe, tare da neman sauƙi ga al'umma da fatan alheri."
Sanarwar ta nemi ƴan Nijeriya su guji ɗaukar saƙon da ba daga kamfanin ya fito ba kai-tsaye, tare da guje wa yaɗa jita-jita.