Rundunar ‘yan Sandan Babban Birnin Nijeriya Abuja ta ce wani abu da ake kyautata zaton bam ne ya tashi a wata makarantar Islamiyya a ƙauyen Kuchibuyi da ke yankin Bwari a bababban birnin ranar Litinin, inda ya yi ajalin mutane biyu
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Josephine Adeh ta fitar ranar Litinin, ta ce wasu mutum biyun kuma sun ji rauni, cikin har da wata mata da ke sayar da kayayyaki.
Sanarwar ta ce ana zargin wasu mutane ne uku da suka ziyarci mai makarantar ne suka je da bam ɗin tsangagyar ta Malam Sani Uthman da ke ƙauyen na Kuchibuyi, inda ya tashi da su, ya yi ajalin biyu daga cikinsu, yayin da na ukun kuma ya jikkata.
SP Josephine ta ƙara da cewa binciken farko-farko da aka yi ya tabbatar da cewa bam ne ya tashi, domin an samu ɓaraguzansa a wajen.
Ta kuma ƙara da cewa tuni aka kam mai makarantar domin yi masa tambayoyi.