Dakarun sojin duka ƙasashen biyu suna aiwatar da ayyukan haɗin gwiwa don dakatar da hare-haren da ake fama da su. Hoto: Getty Images

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun sanar da cewa sun kama wani babban shugaban 'yan bindiga da ke da hannu a sace da kashe fararen hula a Nijeriya tare da yaransa 65 a kudancin ƙasar.

An shafe tsawon shekaru 'yan bindiga suna samun mafaka a yankunan da ke kan iyakar Nijeriya da Nijar, inda suke kashe mutane da sace su don karɓar kuɗin fansa.

"Bayan shafe kwanaki ana bibiyarsa, jami'an rundunar da ke yaƙi da ta'addanci sun kama fitaccen ɗan bindigar nan (Kachalla) Baleri da wasu yaransa," kamar yadda gwamnan yankin Issoufou Mamane ya faɗa a gidan talabijin na ƙasar a ranar Laraba da marece.

A wani bidiyo da gidan talabijin ɗin ya nuna an ga mutanen zaune a ƙasa fuskokinsu a rufe, inda tashar ta ce an kama su ne da tsakar rana "suna tsaka da yin wani taro na shirya kai hare-hare a kan dakarun tsaro."

Mutanen da ake nema ruwa-a-jallo

Gwamnan yankin Maradi ya ce Baleri, wanda ɗan asalin jihar Zamfara ne, shi ne mutum na 40 a jerin mutanen da rundunar sojin Nijeriya ke nema ruwa-a-jallo.

A cewar gidan talabijin ɗin, Baleri yana da hannu "a hare-hare da dama a Nijeriya", har ma da wani mummunan harin da aka kai ranar 22 ga watan Fabrairu inda aka kashe sojoji huɗu.

"Masu fyaɗe ne, ɓarayi ne, masu satar dabbobi ne, kuma masu kisan gilla ne," in ji alkalin Babbar Kotun Maradi Adam Adamou.

Dakarun sojin duka ƙasashen biyu suna aiwatar da ayyukan haɗin gwiwa don dakatar da hare-haren.

AFP