President Bola Tinubu

Fadar Shugaban Nijeriya ta yi magana a kan ƙudurin dokar haraji da ake ta ce-ce-ku-ce a kanta a cikin makonnin nan, inda a ranar Litinin ta ce ƙudurin bai ƙunshi batun soke hukumomi irin su TETFUND da NASENI da NITDA ba.

A sanarwar da Fadar Shugaban Kasar ta fitar mai dauke da sa hannun mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai Bayo Onanuga, ta ce a maimakon haka, sauye-sauyen na da nufin daidaita tsarin harajin Nijeriya, da rage nauyi a kan ‘yan kasuwa da kuma bunƙasa zuba jari.

Tun bayan da batun ƙudurin sabuwar dokar harajin ya bayyana, ‘yan ƙasar suke ta muhawara kan alfanunta da kuma akasin haka.

Amma sanarwar Fadar Shugaban Kasa ta jaddada cewa kudurorin sun rage biyan haraji gutsul-gutsul zuwa a dunƙule don tabbatar da cewa hukumomi sun ci gaba da samun kudade ta hanyar tanadin kasafin kudi.

Sauye-sauyen, in ji Onanuga, an tsara su ne don sabunta dokokin haraji da suka tsufa, tare da haɓaka ci gaban ƙasa ba tare da an talauta kowane yanki ba.

Sanarwar ta kara da cewa: “Kudirin sake fasalin haraji ba zai sa Legas ko Ribas su fi sauran jihohin kasar wadata ba, kamar yadda ake yayatawa. Kudirin ba zai lalata tattalin arzikin kowane sashe na kasar ba.

“A maimakon haka, suna da burin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, musamman ma marasa galihu, wadanda ke kokarin samun abin rufin asiri. Sabanin karyar da ake yadawa, kudurorin ba su nuna cewa za a rushe hukumomi irin su NASENI,da TETFUND, da NITDA ba nan da shekarar 2029 bayan an zartar da kudirin.

TRT Afrika