Heineken Lokpobiri ya ce ba gwamnati ce ke saka farashi ba, kuma kwanan nan farashin zai daidaita da zarar man ya wadata. Hoto:  Reuters

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce babu hannunta aƙarin farashin man fetur da aka samu a farkon makon nan, bayan da aka wayi garin Talata gidajen mai na NNPC suka sa sabon farashin lita a ƙasar.

Sabon farashin litar man ya koma daga tsakanin naira 855 zuwa 897 a wurare daban-daban a gidajen man NNPCL, daga tsohon farashinsa na naira 568 zuwa 617.

A wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida a Fadar Aso Rock bayan ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Ƙaramin Ministan Man Fetur Sanata Heineken Lokpobiri ya tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa nan ba da daɗewa ba wahalar mai za ta zama tarihi a Nijeriya.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya kira Ƙaramin Ministan Man Fetur da Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa NNPCL, Mele Kyari da ma Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro Mallam Nuhu Ribadu a ranar Alhamis, don tattaunawa kan batun farashin fetur din da ‘yan Nijeriya ke ta ƙorafi a kai.

Minista Lokpobiri ya ce Shettima ya kira taron ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce ta damu matuƙa a kan wahalhalun da talakawan ƙasar ke fuskanta.

Sannan ministan ya ce ba gwamnati ce ke saka farashi ba, kuma kwanan nan farashin zai daidaita da zarar man ya wadata.

"Abu mafi muhimmanci shi ne cewa akwai man nan a ƙasar nan, kuma mun yi amanna cewa daga yanzu zuwa ƙarshen mako, za a samu wadatarsa sosai a faɗin ƙasar.

“Farashin ka iya yin tsada sosai a wasu yankunan fiye da wasu. Amma idan har man ya wadata a fadin ƙasar, to zai daidaita kansa.

“Amma abu mafi muhimmanci dai shi ne gwamnati ba ta saka farashi. Kuma yana da kyau ‘yan Nijeriya su san hakan,” a cewar Lokpobiri.

Ya kuma jaddada cewa ‘yan Nijeroya su daina fargabar sayen man fetur din, “don shi ma yana sa a ga kamar yana wahala bayan akwai wadatarsa.”

Ƙarin kudin man ke da wuya sai farashin ababen hawa ya yi tashin gwauron zabi a wurare da dama a fadin kasar.

TRT Afrika