Tinubu da Shettima sun fita kasashen waje a lokaci guda: Hoto / Fadar Shugaban Nijeriya

Fadar shugaban ƙasa a Nijeriya ta yi ƙarin haske game da fitar Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima zuwa ƙasashen waje a lokaci guda, inda ta yi kira ga 'yan ƙasar da su kwantar da hankalinsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga ya fitar ta shafin X, ya yi ƙarin haske game da tambayar da 'yan jarida suke yi game da wanda ke jagorantar ƙasar a halin yanzu, a lokacin da shugaba da mataimakinsa suka fita ƙasashen ƙetare.

Shugaba Tinubu dai ya tafi hutun makonni biyu ne a ƙasar Ingila da kuma Faransa, yayin da a ranar Laraba Kashim Shettima ya tafi Sweden domin halartar wani taro.

Sanarwar ta ce duk da Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ba sa Nijeriya "ya kamata a sani cewar suna gudanar da cikakken aikinsu, kuma babu wani giɓin shugabanci a ƙasar."

Onanuga ya ci gaba da cewa dukkan hukumomin gwamnati na aiki yadda ya kamata, Shugaban Majalisar Dattawa, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ministoci da Shugabannin Hukumomin tsaro na nan a kan mukamansu, don tabbatar da komai ya tafi yadda ake buƙata.

Hasalalima Onaguga ya ce an taɓa samun irin wannan yanayi "a 2022 lokacin da tsohon shugaban Nijeriya Buhari da tsohon mataimakinsa Osinbajo suka bar Nijeriya a lokaci guda. Shugaba Buhari ya halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 77, yayin da Osinbajo ya halarci jana'izar Sarauniya Elizabeth II."

Kazalika, sanarwar ta sake bayar da misalin samun irin wannan yanayi a tsakanin ƙarshen watan Afrilu da farkon watan Mayun wannan shekarar ta 2024, inda Shugaba Tinubu ya tafi Landan bayan ziyartar ƙasashen Netherlands da Saudiyya inda ya halarci Taron Tattalin Arziki na Duniya, shi kuma mataimakinsa Kashim Shettima ya tafi Nairobi don Halartar Taron Shugabannin Ƙasashe na Ƙungiyar Cigaban Ƙasa da Ƙasa (IDA21), bayan ya dawo gida, ya sake tafiya Dallas a Texas don halartar Taron Kasuwanci na Amurka da Afirka.

"A duk wannan lokaci, babu wani aiki na gwamnati da ya tsaya,"a cewar sanarwar.

Sanarwar kakakin shugaban Nijeriyar ta ce "Kundin tsarin mulki na Nijeriya ba ya buƙatar lallai sai shugaban ƙasa da mataimakinsa na nan a zahiri a cikin ƙasa kafin su iya gudanar da ayyukansu."

Ta ƙara da cewa ranar 3 ga Oktoban nan ne Shugaba Bola Tinubu ya tafi hutun makonni biyu. Kuma a wannan yanayi, yana amsa kiran waya tare da bayar da umarni. Inda ta ce nan da wani ɗan lokaci zai koma gida Nijeriya.

A ranar Laraba kuma mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tafi ƙasar Sweden don wakiltar Nijeriya a wani taro.

TRT Afrika