Wata babbar mota ta bi ta kan wasu jama’a masu wucewa a gefen titi da kuma wasu ‘Yan Achaba kusa da iyakar Kenya da Tanzania.
Hukumomi a kasar Kenya sun bayyana cewa akalla mutum goma suka rasu, akwai kuma wasu goman da suka samu rauni a hatsarin da ya faru a ranar Asabar.
Wani kwamandan ‘yan sanda a yankin da lamarin ya faru Mark Wanjala ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan wata babbar hanya a garin Migori.
Ya ce direban ya samu matsalar burki ne wanda hakan ya kai ga motar ta kwace masa.
Kwamandan ya ce an kaddamar da wani aiki na musamman domin ceto wadanda suka makale a karkashin babbar motar kuma ana fargabar adadin wadanda suka rasu zai karu.
Wanjala ya kara da cewa akwai wasu mutum biyu ma da rahotanni suka ce an bige su kan gada sun fada cikin kogi, amma ba a soma kokarin ceto su ba.
Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana wa kafafen watsa labarai na kasar cewa direban yana ta matsa odar motar kafin hatsarin ya faru.
Babbar motar ta yi dakon shinkafa ne inda take hanyar zuwa Isebania, garin da ke kan iyaka da Tanzania.
Bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda jama’a ke ta satar buhunan shinkafa a daidai lokacin da wasu mutane ke makale motar ta danne su.
‘Yan Kenya da dama suna tafiya kauyukansu a lokacin hutun Easter, kuma ana yawan samun hatsari a kan hanyoyi a irin wannan lokaci.
‘Yan sanda sun bukaci masu motoci da su bi a hankali tare da tabbatar da cewa an yi wa motocinsu sabis da kyau kafi su hau hanya domin yin tafiya mai tsawo.